Zan Kawo Karshen Kashe-Kashen Zamfara Cikin Wata Daya - ATIKU ABUBAKAR

Dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya fitar da dubarun da zai dauka domin ganin kawo karshen matsalar tsaro a jahar Zamfara.

A cikin sakon hoton video daya fitar a shafinsa na twitter yace,

“Alummar Jahar Zamfara ina tare daku a cikin wannan yanayin da kuka tsinci kanku a hannun mahara wadanda suke sace dukiyar ku kuma suke kashe maku al’umma tare da barnatar maku da dukiyoyin ku”
Zuciya na tana kadawa sosai akan yanayin da kuka tsinci kanku in addua’an Allah ya kawo maku karshen wannan kashe-kashe da kuma irin wahalar da kuke ciki”

"Ni dan takaran shugabancin Kasar nan ne, ina mai tabbatar ma al’ummar jahar Zamfara cewan idan har kuka zabe ni a matsayin shugaban Kasa a ranan 16 ga watan February 2019 bazan zarce wata daya ba da shan rantsuwan kama aiki ba zan turo rundunar zaratan jami’an tsaron na sojoji da yan sanda dubu talatin (30.000) domin su fatattaki wadannan yan ta’adan da suke kashe al’umma a Jahar taku."

"A lokacin zaben Ekiti, Shugaba Buhari ya aika da yan sanda dubu talatin 30,000 chan, ni ina mai tabbatar maku cewan tsaron rayukan al’’umma da dukiyoyinsu yafi mani neman tsare wata kujerar siyasa."

Comments

Popular posts from this blog

Dan Sanda Ya Kashe Matasa Biyu A Benin

Minista Sanye Da Kayan Ala'ada