PASTON DAKE TAIMAKA MA ATIKU ABUBAKAR NA MUSAMMAN AKA HARKOKIN KAMPEN DINSHI YA TAFKA ABUN KUNYA

Mai taimaka ma tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria kuma dan takaran shugaban kasa a karkashin jamiyyar PDP a zaben 2019, Pastor Reno Omokri ya sharara ma duniya karya game da mai gidan shi Atiku Abubakar inda yace mai gidan nashi ya kira iyalan marigayi laftanan Ibarhim Sakaba wanda ya rasa ranshi a harin da yan kungiyar Boko Haram suka kaiwa sojoji a matsugunnin su dake Metele a watan daya shude.

Shidai Pastor Reno ya ce mai gidan nashi tsohon mataimakin shugaban kasan, ya kira iyalan marigayin sannan kuma ya sanya hoton wani bidiyo na karya a shafinsa na twitter inda yake kambama Atiku Abubakar a matsayin mutumin daya damu da halin da sojojin kasar nan suke ciki.

Atiku Abubakar dai ya karyata yaron nashi bayan da iyalan Marigayi Ibrahim Sakaba suka musanta cewan babu wani kiran waya da suka amsa daga wurin tsohon mataimakin shugaban kasa.

Daman dai shi wannan pastor Reno Omokri anayi mashi kallon mutumin dake watsa labarun karya a kafofin sadarwan zamani saboda kawai adawan da yakeyi da wannan gwamnatin

Comments

Popular posts from this blog

Minista Sanye Da Kayan Ala'ada

Zan Kawo Karshen Kashe-Kashen Zamfara Cikin Wata Daya - ATIKU ABUBAKAR

Fashin Bakin Jawabin Shugaban Kasa