Wadansu matasa a garin Enugu sun kone motar kampen na APC
Wadansu matasa a garin Enugu sun kone motar kampen na mallakin Jam'iyyar APC kurmus, Dan takara Honourable Benjamin Nvute wanda yayi magana da manema labarai yace "Motar wacce aka lullube da hotunan yan takara Senator Ayogu Eze, Prince Lawrence Ezeh da kuma na shugaban kasa Muhammadu Buhari itace motar da jamiyyar ke amfani da ita wajen ayyukan ta na kampen a karamar hukumar Nkanu"
Motar wacce aka barta wurin mai gyara dauke da wadansu takaddu masu muhimmanci wadanda suka shafi ayuukan jam'iyyar da kuma na kampen, yazo ya tarar da ita a kone kurmus.
A Jahar dai ta Enugu akwai matsalolin yage-yagen hotunan yan takara tare da allunansu wanda haka yasa masan ke nuna tsoron su aka yanayin siyasar ta Jahar Enugu.
Comments
Post a Comment