SIYASAR MU A YAU

Godiya ta tabbata ga Allah Subahanhu wata'ala daya bani ikon yin tsokachi ko ince fadakarwa a bisa abubuwan da suke faruwa ga SIYSAR MU A YAU.
musamman a wannan lokichin da zabe ke kara karatowa a kasarsamu.

Da farko abinda muka fahimta da siyasa shine, kusantar al'umma zuwa ga gwamnati, sannan gwamnati ta san mene matsalar al'ummarta, ta hanyar bamu damar mu zabi mutanen da muke tsammanin sune adilai a tare da mu, domin su shugabanche mu.

to amman KASH!!! Shin wai jamma'a muna-nufin har yanzu bamu fahimchi ko mai-nene SIYASA BA?

shin jama'a har yanzu bamu san adilin daya dace ya jagoranche mu bane?
to ko son zuciya ne da rashin sanin ciwon kai ne ke damun mu?

ya kamata mu chire kwadayi a tare da mu, mu farka daga magagin bracin da muke yi domin musan matsalolin da suke addabarmu. mu kore azzaluman shugabanni daga mulki, mu kori 'yan baradan su da azzaluman da ke goya masu baya, kai da ma duk wani wanda bai kaunan kawo cigaba a kasar mu.

bai kamata ba ga duk mai kishin kasar mu ba a dinga hada baki da shi ana zaluntar talakawa ba,

'Yan uwana mun mayar da SIYASAR MU A YAU kamar saye da sayarwa,
'yan takara na shugabanchi suna zuba ma matsa kudi suna basu kayan maye da tunzura su wajen tayar da fitina a ksa, domin kawai su cimma burinsu na siyasa,
wadansu mu wadanda basu san ciwon kansu ba kuma marasa kisihin kasa, suna sayar da kuri'ansu akan 'yan kudi kalilan wanda ko kudin cifane baza su ishe ka ba.

wanda hakan yasa a duk lokachin da burin dan takar ya cika baya kula da 'YAN CIN MU ballantana MATSALOLIN MU sai dai kokarin ya mayar da abin da ya kashe a wurin kamfen, sannan da kuma ribar da zai samu.
hakan shiya kawo muna lalacewar koma da kuma koma bayan dukan al'amuran mu.

jama'a ya kamata mu san cewa yanzu fa lokachi yayi da zamu zabi shugaban da zai muna shugabanchi na gari, muzabi shugaba ba don abin hannushi ba ko kuma jam'iyarsa ba,
A'a sai dan Adalchin shi da rikon amana, mu kuma nuna rashin 'yardar mu da magudin zabe.

ya kamata mu san cewa yanzu fa kan mage ya waye, duk wanda muka san cewa azzalumi ne, toh karmu bari ya mulke mu, ya kamata mu lura da irin 'yan siyasan-nan masu kwashe muna arziki suna kaiwa wata kasa, masu gyara gidajen su da shiga manyan motochi da auren mataye.

jama'a ya kamat mu dage, mu kori duk wani dan siysa da ya mayar da siyasar mu a mytsayin ksuwanchi, mu daina yarda da shugabanni da basa alheri sai lokachin zabe, mu kori duk wanda baya son cigaban kasarmu, mu yake azzalumai 'yan amshi shatan gwamnati wadanda ake amfani da su wajen taushe hakkin talakawa.

zabi na hannu mu, mu talakawa

Comments

Popular posts from this blog

Minista Sanye Da Kayan Ala'ada

Zan Kawo Karshen Kashe-Kashen Zamfara Cikin Wata Daya - ATIKU ABUBAKAR

Fashin Bakin Jawabin Shugaban Kasa