''Sheikh: Wannan batu yana nan, mu darika ba ma kafirta kowa. Mun dauki kowa musulmi ne, amma su suna kafirta mu don kawai ba mu shiga Izala ba. Mu babu ruwanmu da kafirta wani. Duk wanda ya kira kansa musulmi mun yarda da imaninsa, komai girman dan Izala idan ya kafirta mu to babu ruwanmu da shi. Hatta kafiri idan ya ganmu ya ga musulmi, idan ya ga iyayenmu ya ga musulmi, bai ma san darikarmu ba balle ya jawo ta, bai san Shehu Tijjani ba balle ya zage shi. Kuma kafiri ba ya daura lasifika a coci ya yi mana rajamun kaulasan, haka a mota, don haka muka ce idan dan Izala ya tsaya zabe da wanda ba musulmi ba, aka rasa na uku sai dan Izala to mu wanda ba musulmin ba za mu zaba. Ba don komai ba saboda ba ya kafirta mu kuma yana cin yankanmu. Kuma ba ya zagin iyayenmu da malamanmu, to shi ya sa za mu zabi kirista mu bar dan Izala don bata mana suna da cin mutuncinmu da suke yi, suke kafirtamu.''
Shiekh Dahiru Usman Bauchi na daya daga cikin manyan malaman Wannan kasar, kuma daya daga cikin manyan Shehunnan Darika, Mun dai san cewan Malamai Mgada Annabawa ne, wato sune wadanda nauyin Sanar da Al'umma Addini ya rataya a wuyansu.
A wannan kasar tamu muna da mabiya addinai daban daban, kuma kowane addini na da mabiya wadanda suke da sabanin ra'ayi da kuma ilimi.
A cikin akida ta musulunchi akwai wurin da in aka zo ake mantawa da bamabchi tsakanin Izala da Darika, ko kuma Izala da Shi'a, kai da ma duk wani irin bamachi, sai a rungumi Musulunchi kawai ga baki daya.
a duk lokachin da shugaba ya nuna Akidar sa na muslunchi, wato ya nuna cewan shi mabiyi ne na Izala ko Darika, toh lallai zai samu Matsala a cikin tafiyar da mulkinsa. haka kuma idan mabiya suka tsaya akan cewa sai mai bin akidar su zasu Zaba ya shugabanche su, toh lallai da akwai matsala.
General Muhammadu Buhari dan Takaran Shugabanchin Kasar nan yana da magoya masu yawa a wannan kasar, a cikin su kuwa akwai Musulami da Kirista, kai har da ma wadanda basu da Addini.
a cikin Muslman akwai 'Yan Darki da Izala haka ma a cikin Kiristan akwai 'Yan Catohlic da kuma 'Yan Baptist.
duk burinsu shine su zabi shugaba adili
A Addinan ce mun san cewa duk mai kaunan kafiri to shima kafirin ne, domin kuwa kafiri makiye addinin mu ne kuma makiyin muslunchi ne. babu wani abu da kafiri zai yi wanda zai taimaka ma muslmi, ko kuma ya nuna yana tare da su har in ba muslunchi ya dawo ba.
akwai ayoyi da hadisan manzon Allah da suka yo bayani akan Bambanchin Kafiri da Muslmi, da kuma nuna kauna ga shi kanshi kafirin.
don shugaba ya taimaka ma mabiyansa bai kamata a dinga zarginsa ba.
Comments
Post a Comment