Posts

Showing posts from September, 2012

FATAWOYIN AIKIN HAJJI DA UMRAH DA ZIYARA (1)

FATAWOYIN AIKIN HAJJI DA UMRAH DA ZIYARA (1) Na SHAIKH ABDULWAHAB BIN ABDILLAH ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ ﻭ ﺻﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺍﻟﻜﺮﻳﻢ 1. Tambaya: Menene ma’anar Hajji? Amsa: Ma’anar Hajji a harshen Larabci shine nufin wani abu. Amma ma’anar Hajji a shari’ance shi ne nufin ziyarar dakin Allah (ka’aba), bisa girmamawa, da wasu kebantattun ayyuka (na ibada), a kebantaccen lokaci, kuma a wani kebantaccen wuri 2. Tambaya: Menene falalar aikin Hajji? Amsa: Aikin Hajji yana da falala da yawa. Kadan daga ciki shi ne: · An karbo Hadisi daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) yace, Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Aikin Umrah zuwa wata umrar, yana KanKare zunuban da ke tsakaninsu. Haka kuma Hajji Mabrur , ba shi da sakamako sai aljanna". · Haka kuma an karbo Hadisi daga Ma'iz (Allah Ya yarda da shi) ya ce: An tambayi Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) cewa: Wadanne ayyuka ne suka fi falala? Sai ya ce: "Imani da Allah Shi kadai, s

IMMEDIATE CALL FOR ACTION

IMMEDIATE CALL FOR ACTION - Go to CNN website scroll to right bottom and VOTE - NO - on the poll where they question "Do you defend the decision to publish images of the Prophet Mohammed?" Please Vote NO - Strongly suggest you do it and share this everywhere as well since at the moment the poll is 65% saying YES and 35% saying NO Difference in 1000 votes ...Change the Situation in Minutes .... Now DO This you all Right NOW and Share on your Profiles too... And Plz Don't be shy on sharing it. http://edition.cnn.com/index.html?bgo_source=web.cnnmobile.com&bgo_content=Other&bgo_owner=Other&bgo_section=Other

FILM DIN BATANCI AKAN ADDININMU DA KUMA MANZO TSIRA (S.A.W) WANDA AMERIKAWA SUKA SHIRYA

DAGA KWANITIN GUDANAR DA SHAFIN DR. AHMAD ABUBAKAR GUMI - Mun kawo muku wannan rubutaccen daga Zauren Shawarar Musulunci dake facebook, ta hannun Muhammad Rabiu dake kaduna da kuma Malam Muhammad Alkasin. Saboda haka don Allah mu karantashi a tsanake da kuma kokarin watsashi. Mun gode Sako daga Sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu BATANCI GA MANZON RAHMA (S.A.W) GASKIYAR LAMARI Allah Ta'ala yana cewa a cikin littafinsa mai tsarki: (kamar haka ne muka sanya wa duk wani annabi abokan adawa daga shaidanun mutane da aljannu....). Al-An'am aya ta112 Ya kuma cewa: (kamar haka ne muka sanya duk wani annabi abokan adawa daga cikin masu manyan laifuka..). Al-Furqan aya ta 31 Ya sake cewa a wani gurin: (Kamar haka ne, ba wani manzo da ya zo wa wadanda suke gabaninsu face sun ce, matsafi ne ko mahaukaci). al-Zariyat aya ta 52. Duk wani da yake karanta al-Kur'ani yake kuma fahimtarsa, sannan kuma ya san sirar annabawa, tun daga kan Annabi Nuhu (A.S) har zuwa Annabin rahma (S.A.