FATAWOYIN AIKIN HAJJI DA UMRAH DA ZIYARA (1)

FATAWOYIN AIKIN HAJJI DA UMRAH DA
ZIYARA (1)
Na
SHAIKH ABDULWAHAB BIN ABDILLAH
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ ﻭ ﺻﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺍﻟﻜﺮﻳﻢ
1. Tambaya: Menene ma’anar Hajji?
Amsa: Ma’anar Hajji a harshen Larabci shine
nufin wani abu. Amma ma’anar Hajji a
shari’ance shi ne nufin ziyarar dakin Allah
(ka’aba), bisa girmamawa, da wasu
kebantattun ayyuka (na ibada), a
kebantaccen lokaci, kuma a wani
kebantaccen wuri
2. Tambaya: Menene falalar aikin Hajji?
Amsa: Aikin Hajji yana da falala da yawa.
Kadan daga ciki shi ne:
· An karbo Hadisi daga Abu Huraira (Allah Ya
yarda da shi) yace, Manzon Allah (Sallallahu
alaihi Wasallam) ya ce: "Aikin Umrah zuwa
wata umrar, yana KanKare zunuban da ke
tsakaninsu. Haka kuma Hajji Mabrur , ba shi
da sakamako sai aljanna".
· Haka kuma an karbo Hadisi daga Ma'iz
(Allah Ya yarda da shi) ya ce: An tambayi
Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam)
cewa: Wadanne ayyuka ne suka fi falala? Sai
ya ce: "Imani da Allah Shi kadai, sa’an nan
yaKi don daukaka addinin Allah, sa’an nan
Hajjin da ya kubuta daga sabo, tsakanin Hajji
mabrur da sauran ayyuka kuma, kamar
tsakanin mahudar rana ce da mafadarta".
· A cikin wani Hadisin kuma, Manzon Allah
(Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Mai yaKi
fisabilillahi, da mai aikin Hajji da mai Umrah
dukaninsu tawagar Allah ne. Allah ne Ya kira
su,kuma suka amsa ma Sa, kuma suka roKe
Shi, Ya ba su"
· Haka nan, an karbo daga Nana A’isha (Allah
Ya yarda da ita) ta ce: Na tambayi Manzon
Allah (Sallallahu alaihi Wasallam): Ya
Ma’aikin Allah, shin ko Jihadi ya wajaba a
kan mata? Sai ya ce: "Na'am, Mata suna
jihadi, sai dai babu kisa a cikinsa; shi ne
aikin Hajji da Umrah."
3. Tambaya: Yaushe aikin Hajji yake wajabaa
kan mutum?
Amsa : Aikin Hajji yana wajaba ne a kan
mutum, idan Allah Ya ba shi dama. Damar ita
ce: dukiya, lafiya, amincin hanya da guzuri.
Saboda Allah Madaukakin Sarki Ya ce:
ﻭﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺎ ﺱ ﺣﺞ ﺍﻟﺒﻴﺖ ﻣﻦ ﺍ ﺳﺘﻄﺎ ﻉ ﺍﻟﻴﻪ ﺳﺒﻴﻼ
Ma’ana : "Ubangiji ya wajabta Hajji ga
mutane ga wanda ya samu ikon zuwa a
gareshi"
4. Tambaya: Shin wajibi ne ga wanda Allah
Ya ba shi damar zuwa aikin Hajji ya
gaggauta tafiya ko kuwa zai iya jinkirtawa
zuwa wani lokaci?
Amsa: HaKiKa wanda Allah Ta’ala Ya ba shi
damar aikin Hajji, wajibi ne ya gaggauta
tafiya matuKar babu wani uzuri da zai
hanashi. Kuma ko da yake an samu sabanin
malamai a kan haka, amma wannan shi ne
abin da mafi rinjayen malamai suka tafi a
kai. Daga cikin sahabbai da suka tafi a kan
haka akwai Abdullahi bn Abbas da Abdullahi
bn Umar (Allah ya yarda da su). Haka ma
Imam Malik da Imam Ahmad da Imam Abu
Hanifa da Abu Yusuf duk sun tafi a kai. Ko da
yake Imam Malik yana da fatawoyi guda
biyu, amma wannan ita ce tafi rinjaye. Dalili
kuwa shi ne fadin Allah Ta'ala:
"Ku yi gaggauwa zuwaga neman gafara
daga Ubangijinku …" Da kuma fadarSa:
"Kuma ku yi tsere ga ayyukan alheri ,,,"
Kuma Hadisi ya tabbata daga Abdullahi bn
Abbas (Allah Ya yarda da shi) daga Manzon
Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce:
"Wanda duk ya yi nufin tafiya Hajji, to ya
gaggauta. HaKiKa rashin lafiya zai iya
samunsa ko wata buKata ta bijirro masa." A
cikin wata ruwayar, Ibn Abbas yace: Manzon
Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: "Ku
gaggauta zuwa Hajji (na farilla); haKiKa daya
daga cikinku bai san me zai bijiro masa ba."
Wadannan Ayoyi da Hadisi da muka kawo
ne ke nassanta gaggauta zuwa Hajji,
musamman lafazin, ta yadda ya zo da
umurni tare da kwadaitarwa.

Comments

Popular posts from this blog

Minista Sanye Da Kayan Ala'ada

Zan Kawo Karshen Kashe-Kashen Zamfara Cikin Wata Daya - ATIKU ABUBAKAR

Fashin Bakin Jawabin Shugaban Kasa