FILM DIN BATANCI AKAN ADDININMU DA KUMA MANZO TSIRA (S.A.W) WANDA AMERIKAWA SUKA SHIRYA
DAGA KWANITIN GUDANAR DA SHAFIN DR. AHMAD ABUBAKAR GUMI - Mun kawo muku wannan rubutaccen daga Zauren Shawarar Musulunci dake facebook, ta hannun Muhammad Rabiu dake kaduna da kuma Malam Muhammad Alkasin. Saboda haka don Allah mu karantashi a tsanake da kuma kokarin watsashi. Mun gode
Sako daga Sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu
BATANCI GA MANZON RAHMA (S.A.W)
GASKIYAR LAMARI
Allah Ta'ala yana cewa a cikin littafinsa mai tsarki: (kamar haka ne muka sanya wa duk wani annabi abokan adawa daga shaidanun mutane da aljannu....). Al-An'am aya ta112 Ya kuma cewa: (kamar haka ne muka sanya duk wani annabi abokan adawa daga cikin masu manyan laifuka..). Al-Furqan aya ta 31 Ya sake cewa a wani gurin: (Kamar haka ne, ba wani manzo da ya zo wa wadanda suke gabaninsu face sun ce, matsafi ne ko mahaukaci). al-Zariyat aya ta 52. Duk wani da yake karanta al-Kur'ani yake kuma fahimtarsa, sannan kuma ya san sirar annabawa, tun daga kan Annabi Nuhu (A.S) har zuwa Annabin rahma (S.A.W) to ba zai taba wani mamakin jin cewa makiya Allah da Manzonsa (S.A.W) sun ci zarafinsa ba. Domin Allah ya fada mana cewa haka abin yake tun farkon tarihin annabci a doron kasa, har zuwa cikamakin annabawa (S.A.W).
Ni mamakin da nake yi shi ne na musulmin da za su rika mamakin faruwar hakan, kamar ma ba su karanta Al-Kur'ani ko ba a karanta musu shi suna saurara. Allah ya riga ya fadi cewa hakan zai yi ta faruwa, kuma shin akwai wanda ya fi Allah gaskiyar magana?! Babu. Sirar rayuwar Annabin Rahma (S.A.W) ta gwada mana yadda makiyan musulunci na farko suka yi ta masa kazafi iri-iri, suka ce masa "marar hankali" ko "boka" ko "matsafi" ko "mawaki", d.s. kamar yadda ayoyi dadama a cikin al-Kur'ani suka karantar da mu. Bayan wannan yahudawa da turwa 'yan ci ranin addini (Orientalists) suka ci gaba da irin wannan salo na cin mutuncin manzon Allah (S.A.W) da musulunci a cikin littattafansu da rubuce-rubucens u. Duk wanda ya san wani abu akan wannan ta'asar ta su ba zai kasa tuno makiya Annabin rahma (S.A.W) ba irin su: - Henri Lammens (1862-1937) marubucin nan dan kasar Belgium. - Carl Brockelmann (1868-1953) mutumen Jamus (German). - Rymond Charles (?) dan kasar Faransa (France). - Gustave Edmund Von Grunbum (1909-1972) dan kasar Austria. har ka gangaro zuwa ga irin la'annan dan Buritaniya din nan dan aslalin Indiya, Salman Rushdie.
Duk wadannan da ire-irensu da yawa sun yi rubuce-rubuce masu yawa, cike da zage-zage da kazafi da karerayi ga Manzo Rahma (S.A.W). Don haka babu wani abin mamaki don sun koma ga yin amfani da hayoyin sadarwa na zamani da amfani da hanyar nishadantarwa ta fina-finai su rika isar da mugun nufinsu da la'ananniyar manufarsu.
GAME DA SABON FIM DIN BATANCI:
Dangane da la'anannen Fim din batanci da ya fito a kasar Amuruka an yi shi ne don wata mummunan manufa wacce ba a bayyanta ba, amma duk wanda ya lura da wadanda aka yi amfani da su da wadanda suka jagoranci hada Fim din da tallata shi zai fahimci wannan boyayyar bakar manufar da ake son cimma. La'anannun da suka jagoranci wannan Fim din sun hada da Moris Sadiq wani tanbatstssen kiristan kasar Masar dan kabilar Qibdawa Marasa yawa a kasar.
Shi wannan la'ananne dan taliki, kwanakin baya can wata kotu ta kasar Masar ta zartar da hukuncin korarsa daga zama dan Masar, saboda laifuffuka manya-manya da aka same shi da su. Shi ne yake kira da lalle a raba kasar ta Masar biyu tsakanin musulmi da 'yan tsirarin kiristan Qibdawa. Sannan yake mika kokon bararsu ga daular Banu Isra'la da cewa ta shiga Masar da yaki don ta ceci Qibdawa daga hannun musulmin masar. Sannnan da tsinannen Faston nan Jerry Jonse mazaunin Florida ta kasar Amuruka wanda a shekar (2010) ya yi barazanar zai kona al-Kur'ani a cocinsa. Shi ne wanda ya fara tallata Fim din a cocinsa tun kafin nuna shi a gidajen silima. Baya ga wadannan sai wanda ya dauki nauyin Fim din kuma ya yi director na Fim din, Sam Bacile wani bayahuden Amuraka. Ya ce ya kashe dalar amuruka milyan 5 da ya samo daga wasu yahudawa 100 don shirya wannan kazamtaccen Fim na shi.
Boyayyen manufar da aka so a cimma ita ce, haddasa tarzoma da tashe-tashen hankula a kasar ta Masar bayan an ga ta fara fita daga mulkin danniya da kama-karya da ta dade a cikinsa shekaru masu yawa, karkashin jagorancin 'yan barandan Yahudu da Turai. An yi zabe kuma wadanda ake ganin cewa masu kishin muslunci ne sun lashe zaben. To shi ne ake son a samu hanyar da kasar za ta hargitse a shiga kashe-kashe da kone-konen dukiyoyi. Aka yi amfani da Qibdawa mazauna Amuruka wajen tsara wannan la'anannen Fim din, sannan aka fassara turancin da aka yi amfani da shi zuwa larabci na Masar. Ka ga idan Musulmin kasar Masar suka gani sai su harzuka su aukawa Qibdawa da kisa da kone-kone.
Daga nan ne kuma sai sojoji wadanda ake zargi da marawa tsohuwar gwamnati baya su fito su yi juyin mulki su kama malamai da masu addini su daure da hujjar dawo da zaman lafiya a kasa. To ka ga hakansu ya cimma ruwa ke nan.
To amma inda Allah ya nuna musu ikonsa sai su mutanen Masar suka farga da wuri, su kansu Qibdawan suka fito fili suka yi Allah wadai da tofin-Allah-tsi ne ga wannan la'annen Fim, sannan suka fito cikin 'yan zanga-zanga tun a karon farko don nuna rasahin amincewarsu da wannan Fim. Kongiyoyin Qibdawa sama da 120 mazauna Amuruka da turai suka fitar da bayanan Allah wadai ga wannan Fim da masu shi. Wannan ya taimaka kwarai wajen dakile mummunar manufar da musu wannan Fim suka shirya.
ME YA KAMATA MU YI
Babu shakka manyar makiyan musulunci na Duniya sun fahimci irin girman da Manzon Allah (S.A.W) yake da shi a zukatan musulmin Duniya tun lokacin da Shedan Salman Rushdie ya rubuta Ayoyin shedaninsa. Sun kula da yadda musulmi suka nuna damuwarsu da bakin cikinsu. Don haka sai suka fahimci cewa duk lokacin da suke son tayarwa da musulmi hankali a Duniya to babu abin da za su yi kamar irin wannan cin zarafin.
To sukan yi farin ciki matuka su ga sun tashi hankalin musulmi, ana kashe-kashe da kone- kone, ba a kasashensu ba, a'a a kasashen su musulmin, tsakaninsu da wadanda suke zaune tare da su, wadanda su ma labari suka ji kamar kowa. Ba su suka yi ba, kuma ba su fito sun goyi baya ba. Bayahude da Bature a yau ba su da wata damuwa don an kashe kowane ne, a ko ina ne, idan har za su cimma wata kazamar manufarsu, kamar yadda Amuruka ta yi sa'adda ta kashe jakadanta na kasar Pakistan don ta cimma burinta na kashe Dhiya'ul Haq shugaban Kasar Pakistan wanda take zargi a lokacin da kishin Mujahidun na kasar Afganistan a shekarer 1988. Don haka babban abin da ya kamata mu yi shi ne:
1- Mu kara imani da yakini da cewa Allah ta'ala shi ne ya aiko da Annabinsa da shiriya da addinin gaskiya don ya ba shi rinjaye a kan kowane addini ko da kafirai ba sa so. kamar yadda ya yi alkawari a cikin suratul Taubah aya ta 33, da Fath aya ta 28, da Saf aya ta9 Kuma Annabi (S.A.W) ya ce: (Lalle wannan addini sai ya shiga duk wani guri da dare da rana suka shiga. kuma Allah ba zai bar wani gida na yunbu ba ko na gashi face ya shigar da shi wannan addini, da izzar mai izza, ko kaskanci mai kaskanci, izzar da Allah zai daukaka musulunci da ita, da kaskancin da zai kaskanta kafirci da shi) Ibn Hibban.
2- Mu dage wajen koyi da halayen Manzon Allah da kankamewa koyarsa da aiki da sunnarsa a al'amuran addininmu da rayuwarmu. Wannan zai kara cusa hashi da baki ciki da damwa a zukatan masu son su raba mu da addininmu.
3- Yin aiki matuka wajen fito da tarihin Manzon Allah da kyawawon halayensa da dabi'unasa da rahamarsa, don wadanda ba a so su san hakikanin wanene Annabi Muhammadu (S.A.W) su sani... Wanda ake yin wannan batanci gareshi, don a hana musu fahimtar hakikaninsa, a haramta musu shiga cikin hasken da ya zo da shi Duniya.
4- Mu koya 'yayanmu da iyalanmu sirar Manzon Allah (S.A.W) da sahabbansa domin ya zamana su tashi da ganin girmansu da martabarsu, wanda hakan zai ba su kariya daga duk wani kokari da mikaya za su yi don su bata su a idanunsu, su rabu da sonsu a zukatansu.
Comments
Post a Comment