Posts

Showing posts from November, 2014

Demokradiyya a kasashen mu na Afrika

Shin dama haka demkorad'iyyar take a sauran kasashen duniya? Kodai a kasashen Afrika ne lamarin yake a haka? Akasarin talakawan 'kasar nan bamu san ko mai nene romon demokra'diyya ba, 'yan tsirarun mutane ne kawai suke chin wannan romon ma Demokradiyya a kasashen mu na Afrika. Idan mukayi duba ga kasar Libya wacce take cikin wani mawuyacin hali a wannan lokacin sanadiyyar Demokradiyyar da kasashen yamma suke ikirarin itace hanya mai cike da walwala da kuma 'yanci, zamu ga wannan Demokradiyyar ta wurga kasar ta Libya cikin wani matsananci hali batare da samun romon da kasashen yamma suke cewa akwai a ciki ba. Tsohon Shugaban Kasar Libyar Muammar Gaddafi yayi ma dukkan daukacin al'ummar kasar abubuwan da suke sunma wuce da akira su da demokradiyya muddun kishin kasa ne da kuma cigaban kasa al'umma ke bukta' amman idan walwala ne ta 'yan tsiraru daga kasashen yamma da kuma bada dama ga 'yan kasa suyi zabe, lallai a wanchan lokacin kasar Libya