Demokradiyya a kasashen mu na Afrika

Shin dama haka demkorad'iyyar take a sauran kasashen duniya?
Kodai a kasashen Afrika ne lamarin yake a haka?

Akasarin talakawan 'kasar nan bamu san ko mai nene romon demokra'diyya ba, 'yan tsirarun mutane ne kawai suke chin wannan romon ma Demokradiyya a kasashen mu na Afrika.

Idan mukayi duba ga kasar Libya wacce take cikin wani mawuyacin hali a wannan lokacin sanadiyyar Demokradiyyar da kasashen yamma suke ikirarin itace hanya mai cike da walwala da kuma 'yanci, zamu ga wannan Demokradiyyar ta wurga kasar ta Libya cikin wani matsananci hali batare da samun romon da kasashen yamma suke cewa akwai a ciki ba.

Tsohon Shugaban Kasar Libyar Muammar Gaddafi yayi ma dukkan daukacin al'ummar kasar abubuwan da suke sunma wuce da akira su da demokradiyya muddun kishin kasa ne da kuma cigaban kasa al'umma ke bukta' amman idan walwala ne ta 'yan tsiraru daga kasashen yamma da kuma bada dama ga 'yan kasa suyi zabe, lallai a wanchan lokacin kasar Libya batada wadannan daman.

Amman sunada cikakken dama da hadin kai da kuma cigaba a cikin jerin kasashen duniya, bama A yankin Afrika kawai ba.
Amman romon demokradiyya da kasashen yamma suke so su 'dandana masu ya zame masu wani abun tashin hankali da rabewar kai a yanzu.


Wannan abunda daya faru a Libya kusan duka haka lamarin yake a sauran kasashen mu na Afrika, Misali kasar Masar.

Idan muka dawo kuma a cikin gidanmu Nigeria zamu tabbatar da lallai gwara shekaranjiya da jiya da kuma yanzu.

Wato a lokutan mulki na soja wanda shine mulkin da kasashen yamma suke gaba dashi a duniya, yafi kawo ma kasashen mu na Afrika kwanciyar hankali da natsuwa, musamman a mu nan Nigeria da zaman lafiya ya gagara a yankunan mu.

Talaka bai ji dadi ba, masu milkin ne kawai ke sheqe ayarsu, wannan shine salon demokradiyya a Afrika.


...akwai cigaba

Comments

Popular posts from this blog

Minista Sanye Da Kayan Ala'ada

Zan Kawo Karshen Kashe-Kashen Zamfara Cikin Wata Daya - ATIKU ABUBAKAR

Fashin Bakin Jawabin Shugaban Kasa