Posts

Showing posts from September, 2013

Taron Mjalisar Dinkin Duniya 68th

Image
A jiya talata ne majalisar dinkin duniya ta bude taronta wanda tasaba yi duk shekara-shekara karo na 68 th a babban ginin majalisar dake birnin New York na kasar America Taron yazo ne dai-dai lokacin da kasashen yamma suke nuna ma kasar Syria yatsa akan zargin da akeyma gwamnatin kasar na amfani da makamai masu guba a yakin basasan da ya kusa kwashe sekaru 3 ana gwabaza da ‘yan tawayen kasar . Akuma   dai dai lokacinda ake ci gaba d a cacar baki tsakanin Amurka da Rasha, kan wanda  za'a azawa alhakin kai hari da makamai masu guba a Syria . Hakanan kuma an fara ganin alamun Iran ta fara sassautowa daga tafarkin fito na fito da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyar  d a ake zargin tana fakewa da  shi ne domin habaka makaman nukiliya. Haka kuma akwai batun yaki da ta’addance da kasahsen duniya suke ikararin sunayi a duniyar, inda wannan zaman yazo dai-dai da lokacin da kungiyar Al-Shabab ta kaddamar da wani hari a birnin nairobi na Kenya. Haka kuma akwai batun ya

Zaluncin Jami'an Tsaro a Abuja

Shin haka zamu cigaba da zuro ido muna kallon kisan da jami'an tsaro keyiwa 'yan uwanmu muslmai Hausa/Fulani da sunan Boko Haram? Satin daya gabata na kalli hoton bidiyon gawar-wakin mutane takwas (8) wadanda jami'an tsaro suka kashe babu gaira babu dalili da sunan cewan wai 'yan kungiyar nan ne mai suna Boko Haram, saboda kawai an gansu Muslmai kuma 'yan arewa. lamarin ya girgiza mani jiki matukar ainun, wadanda aka kase talakwan kasar nan ne kuma 'yan arewa masu neman abunda zasu ci, wadanda suka baro garuruwansu na asali suka zo Abuja domin neman abunda zasu rufa ma kansu asiri kasancewar kasawan gwamnati na ba matasa aikinyi, duk da haka kuma basu tsira daga makircin makiyan arewa ba. mutane tawkwas aka nuna gawansu amman duk da haka sunfi nan, kasancewar akwai wadansu kwance a asibiti inda a canma wadansu suka cika. Jami'an Tsaro kasar mu suna cin karen su ba babbaka akan iri-irin wadannan kisan da suke ma fararin hulla da sunan Boko Haram a jahohi