Taron Mjalisar Dinkin Duniya 68th


A jiya talata ne majalisar dinkin duniya ta bude taronta wanda tasaba yi duk shekara-shekara karo na 68th a babban ginin majalisar dake birnin New York na kasar America
Taron yazo ne dai-dai lokacin da kasashen yamma suke nuna ma kasar Syria yatsa akan zargin da akeyma gwamnatin kasar na amfani da makamai masu guba a yakin basasan da ya kusa kwashe sekaru 3 ana gwabaza da ‘yan tawayen kasar .

" Nukiliya da sauran makaman kare dangi basu da gurbi a tsarin tsaron Iran. Manufar kasarmu ita ce mu kawar da duk wani tsoro ko kuma wata damuwa da ake dashi, a kan shirin nukiliyar Iran na samar da zaman lafiya" .
A kusan duk lokacin da ake wannan taron idan shugaban kasar Iran zaiyi jawabi ilahirin zauren taron yakan ragu ne, yawancin Shugabanin kasashen yamma da mukarabansu sukan fice ne daga zauren taron, kokuma su cire abun fassaran dake kunnensu (translator) domin su nuna ma duniya cewan basu tare da Iran dakuma duk irin abunda zata fada, Isreala da america suna daga cikin kasashen dake fara yin hakan, sai gaya wannan karon sun tsaya a cikin zauren, kuma sun saurari abunda sabon shugaban yake fada kodadai ana ganin cewan shi wannan sabon shugaban zai zo da wata sabuwar canji a harkokin siyasar kasan da sauran kasashen duniya.
haka shima Shugaban Kasar Sudan, Umar Hassan al Bashir, yace babu abinda zai hana shi zuwa taron Majalisar Dinkin Duniya da za’a fara a cikin wannan makon. Shugaban na cikin tarkon kotun duniya, wadda ta nemi a kamo shugaban don fuskantar laifukan yaki, kuma kasar Amurka na daga cikin na gaba gaba wajen ganin an kama al Bashir.
Ko a watanni baya da akayi wani taro na kasashen Africa a Nigeria, kotun duniya taba nigeri sammacin kama shugaba umar Albashir

Mua namu shugaban kasa na Nigeria ba’a barshi a baya ba, inda shima yayi nashi jawabin, inda ya tabo hadinkan duniya akan yake da ta’addacin da kuma talauci da yayi ma kasashen Africa katu-tu.


Comments

Popular posts from this blog

Minista Sanye Da Kayan Ala'ada

Zan Kawo Karshen Kashe-Kashen Zamfara Cikin Wata Daya - ATIKU ABUBAKAR

Fashin Bakin Jawabin Shugaban Kasa