Zaluncin Jami'an Tsaro a Abuja

Shin haka zamu cigaba da zuro ido muna kallon kisan da jami'an tsaro keyiwa 'yan uwanmu muslmai Hausa/Fulani da sunan Boko Haram?

Satin daya gabata na kalli hoton bidiyon gawar-wakin mutane takwas (8) wadanda jami'an tsaro suka kashe babu gaira babu dalili da sunan cewan wai 'yan kungiyar nan ne mai suna Boko Haram, saboda kawai an gansu Muslmai kuma 'yan arewa. lamarin ya girgiza mani jiki matukar ainun, wadanda aka kase talakwan kasar nan ne kuma 'yan arewa masu neman abunda zasu ci, wadanda suka baro garuruwansu na asali suka zo Abuja domin neman abunda zasu rufa ma kansu asiri kasancewar kasawan gwamnati na ba matasa aikinyi, duk da haka kuma basu tsira daga makircin makiyan arewa ba. mutane tawkwas aka nuna gawansu amman duk da haka sunfi nan, kasancewar akwai wadansu kwance a asibiti inda a canma wadansu suka cika.


Jami'an Tsaro kasar mu suna cin karen su ba babbaka akan iri-irin wadannan kisan da suke ma fararin hulla da sunan Boko Haram a jahohin Borno, Yobe, Adamawa da sauran wurarin a nan arewacin Nigeria, kuma a duk lokacin da suka kashe al'umma babsu da wata hujja da suke nuna ma duniya na gaskiyan zargi da kuma kisan mutane da sunan su 'yan Boko Haram ne, kamar yadda suka kasa nuna ma duniya shaidar cewan wadannan bayin Allah da suka kashe a Apo (Abuja) 'yan kungiyar Boko Haram ne, bayaga burin kunya da suke tayi da kuma kame-kame da kokarin binne makamai a wurin da sukayi kisan domin su yaudari sauran duniya da cewan lallai wadanda suka kase 'yan kungiyar Boko Haram ne, a irin bayanin da jami'an tsaron sukeyi kai daga jin maganar tasu kasan babu gaskia a cikinta, dukda karyan da jami'an tsaron kasar nan sukeyi akan zaluncin da sukayi na kashe wadannan bayin Allah, shaidu a Abuja sun karyata jami'an tsaron, kasancewar su wadannan bayin Allah masu neman na kansu ne , ba 'yan zaman kashe wanda bane balle har a ji dadi dangantasu da Boko Haram

Sanata Sahabi Yau Kaura Dan Majalisar Dattawa na Nijeriya daga jihar Zamfara ya fito fili ya kasance muhimmin mutum na farko a Nijeriya wanda ya ziyarci mutanen da suka ji rauni a asibiti tare kuma da yin suka ga Jami'an tsaron dangane da amfani da karfin ikonsu wajen hallaka wasu mutane dake zaune a Apo ta Abuja.
Sanata Yau wanda ake sa ran a gobe ya gabatar da kuduri na neman hukunta duk mai hannu cikin wannan lamari a gaban Majalisar Dattawa.
Haka ma zai nemi da a gayyaci Babban Hafsan Sojojin Nijeriya da Sufeto Janar na Yan Sanda da Daraktan Janar na Hukumar Leken asiri ta SSS domin zuwa gaban Majalisar Dattawa domin amsa tambayoyin da kawo hujjoinsu dangane da tabbatar da cewar wadanda aka kashe suna da alaka da Kungiyar nan ta Boko Haram.
Sanata Yau ya nuna cewar akwai rashin adalci da kaucewa hakkokin bil adama wajen amfani da makami Ana kisan yan kasa ba bisa hakki ko doka ba.
Mafi rinjayen wadanda aka yiwa kisan gillar dai sun fito daga jihohin Zamfara, Katsina, Kano da Yobe Neva Arewacin Nijeriya.
Sanata Sahabi Kaura ya baiyana cewar babban matakin da ya dace tun farko hukumomin tsaro su dauka ga irin wannan lamarin shine tsaurara bincike kamin fara kai hari da kuma gano ainihin wanene yake ciki.
Yace Majalisar Dattawa zata bukaci bayani dangane da wanene yake da gidan kuma minene hujjarsa na amfani da Sojoji wajen kisan gilla ga wadanan mutanen.




Comments

Popular posts from this blog

Minista Sanye Da Kayan Ala'ada

Zan Kawo Karshen Kashe-Kashen Zamfara Cikin Wata Daya - ATIKU ABUBAKAR

Fashin Bakin Jawabin Shugaban Kasa