Ministan matasa da wasanni Barrister Solomon Dalung yayi shiga irin ta ala'ada, waɗansu mabiyan shafukan sada zumunta suna ganin yin wannan shigar tashi a matsayin minista bai dace ba. Amman dai ya kamata jama'a su fahimci cewan ala'ada daban take da rike mukamin minista, duk girman mukamin ka ala'adan ka abun riƙewa ce kuma abar girmamawa, saboda haka masu chachakan minista game da wannan shigan nashi basu kyauta ma ala'adan shi ba sannan basu san girma da muhimmanci al'ada ba.
Dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya fitar da dubarun da zai dauka domin ganin kawo karshen matsalar tsaro a jahar Zamfara. A cikin sakon hoton video daya fitar a shafinsa na twitter yace, “Alummar Jahar Zamfara ina tare daku a cikin wannan yanayin da kuka tsinci kanku a hannun mahara wadanda suke sace dukiyar ku kuma suke kashe maku al’umma tare da barnatar maku da dukiyoyin ku” Zuciya na tana kadawa sosai akan yanayin da kuka tsinci kanku in addua’an Allah ya kawo maku karshen wannan kashe-kashe da kuma irin wahalar da kuke ciki” "Ni dan takaran shugabancin Kasar nan ne, ina mai tabbatar ma al’ummar jahar Zamfara cewan idan har kuka zabe ni a matsayin shugaban Kasa a ranan 16 ga watan February 2019 bazan zarce wata daya ba da shan rantsuwan kama aiki ba zan turo rundunar zaratan jami’an tsaron na sojoji da yan sanda dubu talatin (30.000) domin su fatattaki wadannan yan ta’adan da suke kashe al’umma a Jahar taku." "A lokacin zaben ...
A ciki ‘yan kwanankin nan 'yan Nigeria muna ta daga murya da nuna rashin yardar mu akan bacewar kudi 20B$ daga assusun ma'aikatar man fetur na kasa da kuma nuna rashin yarda akan yara 'yan makaranta masu rubuta jarabawar karshe na secondary da aka sace a garin Chibok na jahar Borno, sai gaya a cikin hirar da shugaban kasa Jonthan yayi da 'yan jaridu a jiya yana cewan "Ban san inda wadannan yaran suke ba, sannan maganar kudi da ake cewan sun bace ban sani ba" Wato ya kasance kenan duk tayar da jijyan wuyoyin da talakawa, iyaye da kuma masu fashin baki suka dingayi a kasar nan ya zamo na Banza kenan, domin kuwa wanda yake shugabantar kasar kuma wanda ya dace ya kasance a sahu na gaba-gaba wajen nemo ma talakwa haqqinsu a kasar nan yayi wannan maganar. Shin a haka zamu cigaba da kasanncewa a tare da irin wannan shugaban wanda bai san nauyin day a rataya a wuyansa ba? A duk inda shugaba ya kasance ana son ya kasance ne wanda dukkanin muhimman abubawan na tafiya...
Comments
Post a Comment