Wani dan sanda da yayi tatul da giya ya kashe waɗansu matasa biyu a wajen murnan shigowar sabuwar shekara, lamarin ya faru ne a Kings square dake Birnin Benin ta Jahar Edo. Shidai jami'in tsaron yazo halba bindiga a sama ne domin murnan shigowar shekarar 2019 amman ya kuskure juya bindigan zuwa sama inda ya samu waɗansu matasa dake wurin ya bindige su, anan take daya daga cikin matasan ya sheka lahira, dayan matashin kuma ya cika ne bayan da aka gaza samun jami'an kula da lafiya da zasu iya bashi taimakon gaggawa.
Dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya fitar da dubarun da zai dauka domin ganin kawo karshen matsalar tsaro a jahar Zamfara. A cikin sakon hoton video daya fitar a shafinsa na twitter yace, “Alummar Jahar Zamfara ina tare daku a cikin wannan yanayin da kuka tsinci kanku a hannun mahara wadanda suke sace dukiyar ku kuma suke kashe maku al’umma tare da barnatar maku da dukiyoyin ku” Zuciya na tana kadawa sosai akan yanayin da kuka tsinci kanku in addua’an Allah ya kawo maku karshen wannan kashe-kashe da kuma irin wahalar da kuke ciki” "Ni dan takaran shugabancin Kasar nan ne, ina mai tabbatar ma al’ummar jahar Zamfara cewan idan har kuka zabe ni a matsayin shugaban Kasa a ranan 16 ga watan February 2019 bazan zarce wata daya ba da shan rantsuwan kama aiki ba zan turo rundunar zaratan jami’an tsaron na sojoji da yan sanda dubu talatin (30.000) domin su fatattaki wadannan yan ta’adan da suke kashe al’umma a Jahar taku." "A lokacin zaben ...
Ban san abunda yan majalisan Jahar Zamfara sukeyi ba da suka kasa tsige gwamnan Jahar. Lamarin tsaro ya tabarbare a Jahar kuma a zahiri gwamnatin Jahar ta kasa kawo karshen matsalar duk dayake wasu mutane laifin gwamnatin tarayya suke gani akan matsalar, amman masu dora kasawa akan gwamnatin tarayya ya kamata suyi nazari akan hakkin daya rataya akan kowace gwamnati tun daga matakin karamar hukuma har zuwa ga jaha dana tarayya. Gwamna Abdulaziz Yari bashida tausayin talakawan shi, bashida kishin Jahar shi balle har yaso cigaban ta kuma abun takaici ma wai shine shugaban gwamnoni ƙasar nan, kaico!
Comments
Post a Comment