Posts

Showing posts from 2018

Mata (11,0000) Yan Najeriya Ke Karuwanci A Kasar Italiya

Image
Kimanin yan mata matasa dubu goma sha daya (11,0000) aka tsallaka dasu kasar Italiya domin yin aikin karuwanci a shekarar 2016 kawai, wannan kiyatsin ya fito ne daga jaridar Economist, ta wallafa wannan adadin ne a shafinta na twitter. Sau dayawa dai ana fitar da yan mata matasa zuwa kasashen ketare da sunan nema masu ayyukan yi inda akarshe ake ake saka su a hanyar karuwanci da kuma bauta.

Minista Sanye Da Kayan Ala'ada

Image
Ministan matasa da wasanni Barrister Solomon Dalung yayi shiga irin ta ala'ada, waɗansu mabiyan shafukan sada zumunta suna ganin yin wannan shigar tashi a matsayin minista bai dace ba. Amman dai ya kamata jama'a su fahimci cewan ala'ada daban take da rike mukamin minista, duk girman mukamin ka ala'adan ka abun riƙewa ce kuma abar girmamawa, saboda haka masu chachakan minista game da wannan shigan nashi basu kyauta ma ala'adan shi ba sannan basu san girma da muhimmanci al'ada ba.

Tsohon Shugaban Kasar Nigeria Alhaji Shehu Shagari Ya Rasu

Image
Allah yayi ma tsohon shugaban ƙasa Nigeria Alhaji Shehu Shagari rasuwa a yau juma'a a asibitin tarayya dake Birnin Abuja, ya rasu yanada shekaru 93 a duniya. Gwamnan Jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ne ya sanar da mutuwan tsohon shugaban kasan a shafin sa na Twitter. Allah ya jikanshi da rahamarsa.

Zan Kawo Karshen Kashe-Kashen Zamfara Cikin Wata Daya - ATIKU ABUBAKAR

Image
Dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya fitar da dubarun da zai dauka domin ganin kawo karshen matsalar tsaro a jahar Zamfara. A cikin sakon hoton video daya fitar a shafinsa na twitter yace, “Alummar Jahar Zamfara ina tare daku a cikin wannan yanayin da kuka tsinci kanku a hannun mahara wadanda suke sace dukiyar ku kuma suke kashe maku al’umma tare da barnatar maku da dukiyoyin ku” Zuciya na tana kadawa sosai akan yanayin da kuka tsinci kanku in addua’an Allah ya kawo maku karshen wannan kashe-kashe da kuma irin wahalar da kuke ciki” "Ni dan takaran shugabancin Kasar nan ne, ina mai tabbatar ma al’ummar jahar Zamfara cewan idan har kuka zabe ni a matsayin shugaban Kasa a ranan 16 ga watan February 2019 bazan zarce wata daya ba da shan rantsuwan kama aiki ba zan turo rundunar zaratan jami’an tsaron na sojoji da yan sanda dubu talatin (30.000) domin su fatattaki wadannan yan ta’adan da suke kashe al’umma a Jahar taku." "A lokacin zaben ...

Wadansu matasa a garin Enugu sun kone motar kampen na APC

Image
Wadansu matasa a garin Enugu sun kone motar kampen na mallakin Jam'iyyar APC kurmus, Dan takara Honourable Benjamin Nvute wanda yayi magana da manema labarai yace "Motar wacce aka lullube da hotunan yan takara Senator Ayogu Eze, Prince Lawrence Ezeh da kuma na shugaban kasa Muhammadu Buhari itace motar da jamiyyar ke amfani da ita wajen ayyukan ta na kampen a karamar hukumar Nkanu" Motar wacce aka barta wurin mai gyara dauke da wadansu takaddu masu muhimmanci wadanda suka shafi ayuukan jam'iyyar da kuma na kampen, yazo ya tarar da ita a kone kurmus. A Jahar dai ta Enugu akwai matsalolin yage-yagen hotunan yan takara tare da allunansu wanda haka yasa masan ke nuna tsoron su aka yanayin siyasar ta Jahar Enugu.

Akwai Yaruka (Languages) fiye da 507 a Nigeria

Image
Ko kunsan cewan akwai Yaruka fiye da dari biyar da bakwai a Nigeria? A cikin jerin wadannan yrukan, ga guda goma sha biyar wadanda akafi yawan amfani dasu a Nigeria sune - 1-Hausa 2-Igbo 3-Yoruba 4-Fulfulde 5-Kanuri 6-Ijaw 7-Urhobo 8-Efik 9-Edo 10-Tiv 11-Ibibio 12-Igala 13-Ebira 14-Itsekiri 15-Nupe

Gwamnan Jahar Zamfara Abdulaziz Yari Bashida Tausayi

Image
Ban san abunda yan majalisan Jahar Zamfara sukeyi ba da suka kasa tsige gwamnan Jahar. Lamarin tsaro ya tabarbare a Jahar kuma a zahiri gwamnatin Jahar ta kasa kawo karshen matsalar duk dayake wasu mutane laifin gwamnatin tarayya suke gani akan matsalar, amman masu dora kasawa akan gwamnatin tarayya ya kamata suyi nazari akan hakkin daya rataya akan kowace gwamnati tun daga matakin karamar hukuma har zuwa ga jaha dana tarayya. Gwamna Abdulaziz Yari bashida tausayin talakawan shi, bashida kishin Jahar shi balle har yaso cigaban ta kuma abun takaici ma wai shine shugaban gwamnoni ƙasar nan, kaico!

Bishiyar Kirsimati A Cikin Masallaci

Image
Bishiyar kirsimati a cikin masallaci, shin hakan bai saba ma addini muslunci ba? Mundai san Annabi Isah Annabin Allah ne kuma muslamai duka na duniya munyi imani dashi kuma muna grimama shi tare da nuna mashi kauna, amman yaya matsayin yin murnan ranan Haihuwar shi a cikin masalaci?

Gangamin 2023 - Shin Kuna Ganin Hadin Yemi Osinbanjo Da Nasiru El-Rufai Zai Yi Daidai?

Image
Mainene Ra'ayinku idan aka nemi shawaranku game da wanda Buhari zai mika ma mulki idan wa'adin shi ya cika?

ZABEN 2019 - Gangamin Matasa Miliyan Daya Magoya Bayan APC A Jahar Gombe

Image
A jahar Gombe, kungiyar matasan jamiyyar APC sunyi gangame tare da yin alwashin samar ma jamiyyar kuri'u miliyan daya ga shugaba Muhammadu Buhari da kuma dan takaran Gwamnan Jahar Muhammadu Innuwa Yahaya.

KYAKKYAWAN JARUMAR KUDANCI NIGERIA TA NOLLYWOOD

Image
Ini Edo Jarumar shirya fina-finan kudancin kasar nan na Kannywood sanya da jajayen tufafi , kanya sun kayatar.

PASTON DAKE TAIMAKA MA ATIKU ABUBAKAR NA MUSAMMAN AKA HARKOKIN KAMPEN DINSHI YA TAFKA ABUN KUNYA

Image
Mai taimaka ma tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria kuma dan takaran shugaban kasa a karkashin jamiyyar PDP a zaben 2019, Pastor Reno Omokri ya sharara ma duniya karya game da mai gidan shi Atiku Abubakar inda yace mai gidan nashi ya kira iyalan marigayi laftanan Ibarhim Sakaba wanda ya rasa ranshi a harin da yan kungiyar Boko Haram suka kaiwa sojoji a matsugunnin su dake Metele a watan daya shude. Shidai Pastor Reno ya ce mai gidan nashi tsohon mataimakin shugaban kasan, ya kira iyalan marigayin sannan kuma ya sanya hoton wani bidiyo na karya a shafinsa na twitter inda yake kambama Atiku Abubakar a matsayin mutumin daya damu da halin da sojojin kasar nan suke ciki. Atiku Abubakar dai ya karyata yaron nashi bayan da iyalan Marigayi Ibrahim Sakaba suka musanta cewan babu wani kiran waya da suka amsa daga wurin tsohon mataimakin shugaban kasa. Daman dai shi wannan pastor Reno Omokri anayi mashi kallon mutumin dake watsa labarun karya a kafofin sadarwan zamani saboda kawai adawa...

Jahar Zamfara

Image
Maganar gaskiya abunda ke faruwa a jahar Zamfara babban abun takaici ne da kuma rashin imani, a Jahar Zamfara kisan gilla da akeyi ma al'umma ya zama kamar wani abun da aka saba na yau da kullum, munsan cewan gwamnati na yin kokari wajen kawo karshen matsalar nan, amman duk da haka muna kira da babban murya akan gwamnati ta kara zage damtse wajen kawo karshin wannan kisan gillan da yan ta'adda keyima talakawa. Shin mainene kokarin da ministan tsaron kasar nan yakeyi ma jahar sa ta Zamfara domin kawo karshen kisan gillan da akeyi ma mutaenen shi? Mnasur Dan-Ali mai ritaya sam bamu ga amfaninka ga alummar jahar Zamfara ba kuma abun kunya ne gareka ace ka kasa kawo karshen kisan gillan da akeyi ma al'ummar ka, idan ka kasa yin tsayin daka domin kare al'ummar ka mainene kakeso ka saka masu dashi? Manyan mutanen da suke yan asalin Jahar Zamfara musamman wadanda ke cikin gwamnati, baku kyauta ma wannan jahar taku ba musamman talakawanku, domin kun tsallake kun barsu kun...

ATIKU ABUBAKAR YA BUKACI YAN NIGERIA SU NUNA MA YAN UWA KAUNA A LOKACIN BUKIN KIRSIMATI

Image
Dan Takaran Shugaban Kasar Nigeria a karkashin innuwar jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci Yan Nigeria da su nuna ma yan uwa so da kauna a lokacin bukin Kirsimati a sakon da ya isar ma al'ummar Kirista a ranan Litinin domin tayasu murnar wannan ranan.

Wani matashi ya rasu sati ukku kafin auren shi

Image
Wani matashi mai Adejoh (Kamar yadda abokin shi ya wallafa a shafinsa na Facebook) ya rasu sati ukku kafin daurin auren shi da budurwarsa mai suna Jamila Muhammed, Matashin dai dan garin Ankpa ne dake Jahar Kogi. Allah ya jikanshi da rahama.

Tips for safe banking during festive season

During the festive season, there is a need to empower people with information to ensure that they bank safely, according to https://www.sanews.gov.za. SABRIC says fraudsters take advantage of the fact that consumers receive bonuses, spend more money and are generally more relaxed because they are in holiday mode. The festive season typically sees an increase in the use of online banking and card transactions and it urged bank clients to take note of the latest crime trends so that they do not become victims. Although, the advent of digital technology has seen an increase in electronic banking crimes, SABRIC still urged consumers to remain aware of other modus operandi at play, such as card fraud and phishing, both of which are on the increase. By interrupting or interfering with a bank client while he or she is transacting, cards are stolen, swopped or trapped in the ATM to be retrieved later by the fraudster. “By covering the PIN when punching in the numbers, bank clients wi...