Rashin Adalcin Duniya (2)
Rashin Adalcin Duniya (2)
Idan mukayi duba akan lamarin satar yara 'yan makaranta da kungiyar Boko Haram ta sace su kusan 200 da 'yankai, inda hankali duniya ya karkata kan gwamnatin Nigeria domin ganin an ceeto wadannan yaran, inda har gwamnatin kasar mu Nigeria tayi tayin neman taimako daga manyan kasashen duniya kan ceto wadannan yaran 'yan makaranta.
Duk dayake lamarin daya shafi tsaro lamari ne dake bukatan taka tsan-tsan da kuma boye wadansu surruka tare da amfani da kwararun jami'ai.
Toh babban abundake daure mani kai shine yadda gangamin kungiyoyi ke fuskanta barazana a nan cikin gida Nigeria tare kuma da lafawar yawan gangamin da kungiyoyi ke shiryawa kan gwamnati takara matsa kaimi wajen ceto wadannan yaran.
Kungiyar #BringBackOurGirls ta fuskanci barazana da wata kungiyar mai suna irin nata a Unity fourtune Abuja, wurin da suke taruwa domin isar ma gwamnati da sakon su, Inda lamarin ke daure mani kai akan ceewan su wadannan kungiyoyi idan har don Allah sukeyi toh mai nene na yunkurin kawo tashin hankali ga takwarorinsu? Kodai akwai kungiyar #BringBackOurGirls ta 'yan kwangila ne?
Babba lamarin rashin adalcin duniya shine yadda aka bari har gwamnati take alakanta duk wani gazawanta akan jam'iyyar adawa batare da duniya ta hankaltar da gwamnatin namu ba, musamman ma wannan gangamin na 'yan #BringBackOurGirls da gwamnatin ke alakantawa da cewar kungiya ce ta siyasa kuma ta 'yan adawa.
Ya kamata jama'ar Nigeria mu lura cewan a lamarin daya shafi kasa ga baki daya bai kamata gwamnati ta ringa nuna zargi na siyasa a cikinsa ba, bai kuma dace a kullum idan gwamnati ta kasa ba ta ringa nuna kasawanta akan matsala ce data koma siyasa, musamman sha'anin tsaro daya sukurkunci a wannan kasar tamu.
Akawai kasawa na gwamnatin kasar nan tamu kan rashin mayarda hankali wajen kubutar da 'yan makaranta #Chibok, kasancewar gwamnati ce keda sojoji, sukeda SSS haka kuma sukeda 'yan sanda, amman saboda Rashin Adalci na duniya sai kaji wadansu na danganta rashin kasawar ga gwamnatin jahohin da abin ya shafa.
Lamarin yanada ban haushi matuka da kuma tausayi, musamman idan muka dubi halin da iyayen wadannan yaran suka shiga na rasa yaransu a kusa dasu, duk dayake duniya ta nuna cewan tana tare da Nigeria, toh amman da gaske ne duniyan tana tare damu?
Toh idan hard a gaske ne ya akayi lamarin ya fara sanyi duk da sojojin da wadansu kasashe suka turo a Nigeria domin kubutar da yaran?
Kar mu manta fad a jirgin saman kasar Malysia da yayi batar dabo a cikin sararin samaniyyar nan, inda ‘yan uwa tare da iyayen fasinjojin dake cikin jirgin suka dinga gangami domin ganin duniya ta taimaka wajen gano wannan jirgin kokuma halin da ‘yan uwansu suke a ciki, duk da hadin kai da duniyar ta bayar a yanzu dai lamarin shiru kakejinsa, babu wani tsayayen Magana dake fitowa daga gwamnatin kasar Malysia bare kuma har kafafen yada labrai na duniya su yada.
Toh haka lamarin #BringBackOurGirls ya keson komawa a Nigeria, duk dayake an san hannun da yaran suke, amman lamarin kubutar dasu babu wani tsayayen Magana daga bakin sojojin kasar tamu, duk dayake sun fitar da jawabin cewan sun san inda wadannan yaran suke, amman bazasuyi amafni da karfin soji ba wajen kubutar dasu ba.
Kafafen yada labara na duniya su kansu a yanzu abun ya soma sanyi wajen su, sun riga sun gama chin ribarus da wannan babban labarin, anbar iyayen yara a cikin tunani.
Ko a wanchan satin daya gabata daya daga cikin iyayen yaran nan ya rasa ranshi sanadiyyar bugun zuciya da kuma tunani, amman duniya tayi shiru akan wannan mutuwar ta wannan bawan Allah, bayan kuma kazawar duniya ta janyo sanadiyyar mutuwarsa.
A karshe dai ina addu’an Allah ya kawo muna gwamnati mai adalci a kasar nan, Allah kuma ya tausaya muna a halin da kasar nana tamu take ciki. Allah ya kubutar damu daga hannun masheranta.
Aameeen.

Comments
Post a Comment