#BringBackOurGirls
Tun lokacin da aka sace yara nan 'yan makaranta banji wani bayani tsayaye daga bakin jam'ian tsaro ba ko kuma daga fadar shugaban kasa ba.
Iyakaci kawai iyaye yaran ne kawai ke naso kokarin ganin sun samu bayanai da kansu, duk da irin matsa kaimi dda jama'a da kuma kungiyoyi keyi a kasar nan dama duniya baki daya.
A karshe dai munji cewan jami'an tsaro na kasar America zasu kawowa Nigeria dauki domin ganin an gano su wadannan yaran da aka sace.
Toh ni abubwa dake daure mani kai sannan nake ganinsu da alamun tambaya sune:
Shin sauran yaran nan da suka samu tserewa daga hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram basuyi magana da wata kafar yada labari bane? Domin nidai banji wata hira da akayi da daya daga cikin yaran da aka sacen suka samu daman kubuta ba.
Sannan a duk inda ake bincike abunda ya bace akan bi sawun wata alamu da aka gani imma sawun inda abunda ya bace yabi kokuma wane bayani da aka samu gamsashe, Toh shin wadannan yaran da Allah yasa suka kubuta basu samu daman baiwa jami'an tsaro bayanai banee game da inda aka nufa dasu ba da kuma wadansu bayanai masu alaka da sansanin 'yan kungiyar Boko Haram ba?
Shin ta wane bangare ne jami'an tsaron mu suka kasa?
Rashin kayan aiki ne kokuma rashin kwarewa ne?
Mai nene makomar manyan jami'ian tsaron namu dasuka kasa? Da kuma dumbin dukiyar da ake ware masu?
Ya kamata mu samu cikakken bayani akan wannan lamarin ba wai a dinga yi muna jawabi a dunkule ba.
Jawabi mai ma'ana kamar yadda yake faruwa a kasar Malysia na bacewar jirgin sama.
Minista Sanye Da Kayan Ala'ada
Ministan matasa da wasanni Barrister Solomon Dalung yayi shiga irin ta ala'ada, waɗansu mabiyan shafukan sada zumunta suna ganin yin wannan shigar tashi a matsayin minista bai dace ba. Amman dai ya kamata jama'a su fahimci cewan ala'ada daban take da rike mukamin minista, duk girman mukamin ka ala'adan ka abun riƙewa ce kuma abar girmamawa, saboda haka masu chachakan minista game da wannan shigan nashi basu kyauta ma ala'adan shi ba sannan basu san girma da muhimmanci al'ada ba.
Comments
Post a Comment