Fashin Bakin Jawabin Shugaban Kasa
A ciki ‘yan kwanankin nan 'yan Nigeria muna ta daga murya da nuna rashin yardar mu akan bacewar kudi 20B$ daga assusun ma'aikatar man fetur na kasa da kuma nuna rashin yarda akan yara 'yan makaranta masu rubuta jarabawar karshe na secondary da aka sace a garin Chibok na jahar Borno, sai gaya a cikin hirar da shugaban kasa Jonthan yayi da 'yan jaridu a jiya yana cewan
"Ban san inda wadannan yaran suke ba, sannan maganar kudi da ake cewan sun bace ban sani ba"
Wato ya kasance kenan duk tayar da jijyan wuyoyin da talakawa, iyaye da kuma masu fashin baki suka dingayi a kasar nan ya zamo na Banza kenan, domin kuwa wanda yake shugabantar kasar kuma wanda ya dace ya kasance a sahu na gaba-gaba wajen nemo ma talakwa haqqinsu a kasar nan yayi wannan maganar.
Shin a haka zamu cigaba da kasanncewa a tare da irin wannan shugaban wanda bai san nauyin day a rataya a wuyansa ba?
A duk inda shugaba ya kasance ana son ya kasance ne wanda dukkanin muhimman abubawan na tafiyar da 'kasa yana kula dasu sosai, kuma yana bin sawon duk abunda ke tafia, sai gaya wannan shugaban namu ya kasance babu ruwanshi da manyan lamurorin da suka sahfi 'yan kasa, babu abunda ya dameshi da damuwan talakawa sannan a duk lokacinn da akayi masa tambaya akan wani muhimmin lamari da ya shafi kasa, sai ya bayar da amsa karkataciya wacce a matsayinshi na shugaba bai dace ya bayar da irin wannan amsar ba.
Idan muk kara duban lamarin yaran nan 'yan makaranta da ake zargin kungiyar Boko Haram ta sace kusan sati ukku da suka gabata, lamari ne Wanda ya dauki hankulan iyayen a kasar nan dama duniya baki daya, sannan lamari ne Wanda ya kamata manyan jami'an tsaro na gwamnatin tarayya su sanya hannu a ciki domin kubutar da yaran da aka sace, sannan lamari ne Wanda ake ganin gwamnatin tarayya ce ya dace tayi ruwa da tsaki akai.
Amman sai gaya shi shugaban kasa da ake kallon zaiyi bayani na gamsuwa yazo da bayani mara ma'ana da kuma rashin nuna kula akan lamarin.
Shugaban kasar namu yayi magana akan kudin 20$B da ake zargin sun bace amman mafi yawancin 'yan kasa ba irin maganar da sukayi tsammanin zata fito bakinshi bane, ya nuna rashin damuwa da kuma kula a lamarin, yayi maganar ne ma kamar baida labari kokuma baima san ainihin yadda maganar take ba.
Shugaban namu kuma yayi maganar neman taimako daga kasashen waje domin yakar ‘yan kungiyar nan ta Boko Haram, inda yake cewa “muna Magana da shugabanin duniya kamar America da France domin yiyuwar su kawo mun dauki wajne yaki da kungiyar Boko Haram”
Shin tamabaya na ga shugaban kasa a nan itace, shin sojojin mu ne suka kasa da har zamu nemi taimako kasashen waje kokuma kayan aiki ne sojojin kasar namu basuda su? Ko dubarun yaki ne basu iya ba?
Karfa mu manta da cewan sojojin mu na Nigeria sun sha zuwa kasashen waje inda ake tashin hankali domin su kwantar da tarzoma tare kuma da koran masu tayar da kayan baya su kuma samu nasara, amman abun mamaki sai gaya sun kasa tabuka komai a cikin gida wai har ana neman taimako daga waje. Saboda haka akwai alamun tambaya a nan ga kan manyan jami’an tsaron kasar nan.
a duk kasashen duniya da ake kaiwa dauki zai yi wuya a gama aikin wanzar da zaman lafia a cikin kankanin lokaci ba tare da an muzguna ma jama’ar kasar ba, wato bakin sojoji wani lokaci sukan takura ma mutanen kasar da suka zo domin wanzar da zaman lafia da kuma kawo masu sababin cututtuka.
Goodluck Jonthan ya kara da cewan masu fafutuka na yankin Niger-Delta mai arzikin man fetur na kasar nan ba ‘yan ta’adda bane, toh tambaya na nan shine idan ba ‘yan ta’adda bane toh waye su?
Marigayi Malam Umaru Musa ‘Yar Adua kafin Allah ya amshi ransa saidai yayi kokari yaga ya dai-daita da ‘yan ta’adda yankin Niger Delta domin samun zaman lafia a yankin, amman shi wannan shugaban namu na yanzu Jonathan y adage akan cewan bazai dai-daita da ‘yan kungiyar Boko Haram ba saboda wai a cewarshi bai sansu ba.
Toh ai koda Marigayi Malam Umaru Musa ‘Yar Adua ya sasanta da Yan Niger Delta bai sansu ba, saida daidaitawan tazo sannan yasan ko su waye su.
Toh shin a haka ake shugabancin kasa? Sannan a haka zamu cigaba da kasancewa dashi har zuwa wani wa'adi da 'yan koranshi keson ya kasance?
A gaskia muna bukata chanji na shugaba, muna bukata Wanda yasan mai ake kira shugabanci, ya kuma san haqqin talakawan sa akanshi, ya kuma san irin maganganun da zai dinga furtawa wadanda yake shugabanta.
Zabi ya rage namu.
Comments
Post a Comment