Rashin Adalcin Duniya (1)
Rashin Adalcin Duniya (1)
Zan soma wannan rubutun mai taken Rashin Adalcin Duniya akan kasarmu Nigeria, musamman lamarin tsaro daya tabar-bare a yankin arewacin kasar nan.
A ko'ina a duniya jama'a sun san da sanin cewan babu wani aiki da zai iyaa gagaran gwamnati, gwamnati kowace kasa kuwa a duniya, idan kuma har wannan aikin ya gagari gwamnati toh dole ne ta tashi ta nemo taimako daga wajen sauran takwarorinta na duniya dommin dakile matsalar datake fuskanta, ganin haka yasa muke ganin babu wani aiki da zai gagare gwamnati kasancewar idan gwamnati daya ta kasa toh akwai masu iya tallafa mata daga wadansu kasashe.
Toh amman kafin gwamnati tace ta kasa har takai ga nemo taimako daga wajen sauran takwarorin ta na duniya toh dole ne sai 'yan kasa sun yaba tare kuma da ganin iyakacin kokarin da gwamnati tayi.
A kasar mu Nigeria jama'a da yawa basu gani ba balle kuma su yaba ma gwamnati kasar tamu ba akan ikirarin datakeyi na yaki da kungiyar ta'addincin nan wato Boko Haram.
A kulum masu yabawa da kokarin gwamnati zaka same su a cikin gwamnati suke ana damawa dasu, amman saboda tsoron fushin ubangidajen su kokuma tsoron kar su rasa kujeransu, sai ka samesu basa son fadin gaskia akan matsalar tabarbarewar tsaro a kasar nan, musamman ma kan wannan kungiyar ta'addancin ta Boko Haram.
A gefe daya kuma wadansu 'yan kasa tare da wadansu jam'ian tsaro suna fadin cewan lallai gwamnati ta kasa kan batun Boko Haram, musamman ma bangaren sojoji da a koda yaushe jama'a ke zargin sunada hannu a cikin rikicin, amman saboda Rashin Adalci irin na wannan Duniyar shi kanshi shugaban kasar tamu ya kasa zakulo wadanda jama'a ke zargi kan batun rikicin musamman ma jami'an tsaron da suke nuna zargi akan manyansu.
Bayan duniya ta shaida cewan gwamnati kasar nan tamu bata tabuka komai ba akan wannan tashin hankalin, a madadin a matsa ma shugaban kasar lamba kan kawo karshen wannan kungiyar sai suma sukace ya dace ne a taimaka ma kasar, domin wai a ganinsu rikicin yafi karfin gwamnati kasar tamu, Bayan kuma a zahiri ba wai so ake a yaki ita kungiyar Boko Haram bane, a'a ana dai kasuwanci ne da rayukan sojojin kasar mu ta sunan yaki da boko haram.
Su kansu kasashen da suka ce sun kawo ma Nigeria dauki akan wannan rikicin na Boko Haram kasuwanci suka shigo suyi a kasar tamu tare da hadin kan shugaban kasar mu, a zahiri kowa yasan cewan duk inda ake yake a Duniyar nan akwai masu cin ribar sa, Ta wannan dalilin yasa a ko'ina cikin duniya tashin hankali baya karewa saboda kawai 'yan kasuwan yaki su ji dadin tafiyar da kasuwancinsu na yaki.
Idan mukayi duba ga wannan rikicin na Boko Haram, idan har da gaske akeyi anason kawo karshen wannan rikicin mai yasa shugabnnin soji basu baiwa mayakanmu makamayan dasuka dace na kuma zamani wajen tinkarar wannan lamarin?
Shin mai nene ya kawo wannan kasha-kashen da akayi a kasar nan da sunan kungiyar Boko Haram?
Shin mai nene ya hana gwamnati murkushe ita wannan kungiyar?
Shin ko akwai wata kungiyar ta’addanci a duniya datafi karfin gwamanti ne a duniyan nan sannan ina kudaden da akae warewa da sunan yakan ita wannan kungiyar suke tafiya?
Mai yasa idan sojojin mu sukaje peacekeeping a wadansu kasashe suke samun nasara?
Shin mai yasa koda yaushe kananan sojoji suke zargin manyansu akan suna iza wutar wannan rikicin?
Mai yasa har yanzu ba'a bayyana ma duniya masu dauke da nauyin wannan kungiyar ba kasancewar akwai masu ikirarin sun sansu?
Mai nene amfanin kama wadanda ake zargi cewan 'yan ta Boko Haram batare da yanke wani hukunci akansu ba kokuma tatso bayanai daga wurinsu ba?
Shin a kasa kamar Nigeria mai ya hana kawo karshen kungiyar kusan shekari biyar kenan?
Idan mukayi duba sosai akan irin makuddan kudaden da gwamnati ke warewa da sunan samar da tsaro a kasar nan lallai akwai lauje cikin nadi na rashin yima ‘yan kasa jawabi akan yadda ake tafiyar da kudin, duk dayake ba kowane bayanai bane akae bayannawa ba, amman ya dace a dinga sanar da ‘yan kasa yanda kasafin kudin tsaro yake tafiya a kasar nan.
Saboda haka dole ne jama'a su farka daga rashin adalcin duniya, duk inda ka samu gwamnati kasa na zaluntar 'yan kasar ta toh akwai hannun wadansu kasashen duniya a ciki wadanda suke cin ribar zaluncin.
Sanna kuma duk wani babban daza’a kama da laifi sai ka samu wandasu manyan kasa da hannu a cikin lamarin, ko manyan cikin gida kokuma na wajen kasashen duniya, inda kuma wannan lamarin ba wai a Nigeria bane kawai haka ke faruwa ba, hard a sauran kasashen duniya baki daya, Saboda haka rashin adalci yayi katutu a duniyar nan.
Duk wata barazana na nuna adalci da sauran kashen yamma suke nuna akan wannan lamarin na Boko Haram yaudara ce kawai suke muna, domin kuwa sune masu cin ribar wannan rikicin.
Dole ne jama'a su san cewa an kafa majalisar dunkin duniya ne (UN) domin shawo kan matsalalin da duniya take ciki, amman kuma a zahiri mun san sun kasa, musamman a yankin mu na Africa.
Comments
Post a Comment