Nigeria!
Nigeria
Lamarin kungiyar ta'addancin da ake kira da Boko Haram tana kawo cikas sosai a lamarin cigaban yankinmu na arewa, sannan kungiyar ta sanya ma yawancin 'yan arewacin kasar nan muslmai zargi a zukatansu kan yadda kungiyar take kashe mutane ba tare da wani haqqi ba da sunan kungiyar addini.
Da dama jama'an arewa sunayi ma kungiyar Boko Haram kallo ta fuskoki da dama.
Wasu nayima kungiyar kallon cewan kungiyar kiristoci ce ta Nigeria ke tafiar da kungiyar domin rage yawan muslman kasar nan.
Wasu kuma nayi mata kallon 'yan siyasa ne ke tafiyar da kungiyar donmin ganin sun cimma burinsu akan zabe mai zuwa na 2015.
Wadanda ke cikin gwamanti da kuma 'yan adawa kowa na daura ma juna laifi akan hare-haren da kungiyar ke kawai da kuma cewan suna daya daga cikin masu tallafawa kungiyar.
Kiristoci dake a gefe kuma sunayi mata kallon kungiya ce ta addini, inda wadansu muslmai masu zafafen ra'ayi suka kafata domin yawa ragen kiristocin dake yankin.
A gefe daya kuma 'yan kasa nayi mata kallon gwamnati ne ke tafiar da kungiyar kasancewa da zaran wani abu mai Jan hankalin 'yan kasa ya faru sai kuma a gefe daya kaji wani hari daga 'yan kungiyar ta Boko Haramn, a cikin sati ukku dasuka gabata an sace wadansu yara 'yan makaranta masu rubuta jarabawar karshe a makarantunsu na kwano dake Chibok a jahar Borono, inda lamarin ya janyo hankulan iyaye da kuma jama'a baki daya na cikin gida da kuma sauran kasashen duniya.
Kungiyoyi masu zaman kansu sunfito sunyi zanga-zanga akan lamarin da kuma nuna rashin Jin dadinsu kan yadda gwamnati ta kasa bayar da cikakkun bayanai akan lamarin tare da yadda jami'an tsaro suka kasa cheto wadannan yaran, kwatsam bayan wannan zanga-zangar limanan da akayi a Abuja sai gaya washi garin ranan bomb ya tashi a babba tashar motoci dake Nyanya a Abuja, inda lamarin ya kara samun daukan hankali daga kasashen duniya sannan kuma lamarin ya daure ma 'yan kasa kai saboda ganin ga yara 'yan makaranta an sace ga kuma Bomb ya tashi a Nyanya ya kuma yi barna mai yawa tare da rasa rayuka.
Duk da haka nan iyaye da kuma kungiyoyi masu zaman kansu basuyi kasa a gwia ba wajen kara yin wata zanga-zangar, inda kuma abunda ya faru a baya ya kara faruwa na tashin wadansu boma-bomai a kuma wurin da suka tashi a wanchan makon daya gabata Wato tashar mota ta Nyanya.
A yau litinin 5/5/2014 Shugaban kungiyar "yan Taddan Boko Haram ya fitar da hoton bidiyo inda yake cewan sune suka sace wadannan yaran.
A jiya lahadi kuma 'yan jaridu sunyi hira da shugaban kasarmu na Nigeria Goodluck Jonthan inda yakecwa bai sain inda yaran nan suke ba, amman zaiyi kokari domin ganin an ceto wadannan yaran.
Tambaya na a nan itace:
Shin mai nene gaskiya Boko Haram wacce take kar-kashe jama'an kasa Muslmai da kirista? Kungiyar kiristoci ce ke dauke da ita kokuma 'yan siyasa, koh kuma kungiyar addini ce?
Wannan amsar ya dace ne ta fito daga bakin wadanda nauyin samar da tsaro ya rataya a wuyansa, ba wai su bar 'yan Nigeria cikin kwo-kwonto ba da zargin juna ba.
Mai yasa a kowane lokaci kungiyar kiristoci suke nuna ma muslmai yatsa akan kungiyar ta Boko Haram sannan suke nuna bam-bamci ga 'yan kasa akan kungiyar?
A shekaran jiya kungiyar kiristoci ta kasa ta fitar da sunayen daliban da aka sace a makaranta 'yan mata dake Chibok, sunayen da ya dace ya fito daga minista ilimi na kasa, sai gashi ya fito daga hannun kungiyar addini, shin kodan mafi yawancin daliban kiritoci ne?
A duk lokacin da akayi kasafin kudin kasa, ana cire ma bangaren tsaro nashi kason, kuma ana cire mashi kaso ne mai tsoka inda ake ware masu madukddan kudade domin ganin sun samar da cikakkun tsaro a kasar amman sai gaya sun kasa.
Wannan alamu kenan na rashin iya shugabanci da kuma rashin kula da haqqin daya rataya akan shugabancin namu musamman jami'ian tsaro na soja, wadanda ake masu kallon suna kasuwanci ne da rayuka jama'a da kuma na 'yan uwansu jami'an tsaron kamar yadda wani jami'in tsaro ya sahidawa wata kafar yada labarai. Toh amman abun mamaki har yanzu babu wani jam'in tsaro da yayi bayanai sosai akan Boko Haram
Shin yaya gaskian kallon da 'yan kasa sukeyima Boko Haram a matsayin a kungiyace wacce 'yan siyasa ke amfani da ita wajen cimma burinsu? Shin akwai alamun gaskia hakan? Saboda tashin boma-bomai a duk lokacin daya 'yan kasa suka fahimci gwamnati tayi ba daidai ba?
Ko a jiya ma jami'ian tsaro sun kama matar dake shugabanta iyayen yaran da aka sace a Chibok bisa ga umurnin Uwar gidan shugaban kasa, kan wani dalili marar ma'ana.
Iyayen yara dai sunyita zanga-zanga da kuma nuna rashin Jin dadinsu kan yadda gwamnati ta kasa da kuma rashin bayyana ma iyayen cikakken bayanai kan yadda lamarin ke tafia.
A karshe dai ina ba 'yan uwana 'yan Nigeria kuma 'yan arewa shawa akan mu tashi tsaye domin ganin mun kawo karshe wannan kungiyar.
Comments
Post a Comment