''Sheikh: Wannan batu yana nan, mu darika ba ma kafirta kowa. Mun dauki kowa musulmi ne, amma su suna kafirta mu don kawai ba mu shiga Izala ba. Mu babu ruwanmu da kafirta wani. Duk wanda ya kira kansa musulmi mun yarda da imaninsa, komai girman dan Izala idan ya kafirta mu to babu ruwanmu da shi. Hatta kafiri idan ya ganmu ya ga musulmi, idan ya ga iyayenmu ya ga musulmi, bai ma san darikarmu ba balle ya jawo ta, bai san Shehu Tijjani ba balle ya zage shi. Kuma kafiri ba ya daura lasifika a coci ya yi mana rajamun kaulasan, haka a mota, don haka muka ce idan dan Izala ya tsaya zabe da wanda ba musulmi ba, aka rasa na uku sai dan Izala to mu wanda ba musulmin ba za mu zaba. Ba don komai ba saboda ba ya kafirta mu kuma yana cin yankanmu. Kuma ba ya zagin iyayenmu da malamanmu, to shi ya sa za mu zabi kirista mu bar dan Izala don bata mana suna da cin mutuncinmu da suke yi, suke kafirtamu.'' Shiekh Dahiru Usman Bauchi na daya daga cikin manyan malaman Wannan kasar, ...