Minista Sanye Da Kayan Ala'ada
Ministan matasa da wasanni Barrister Solomon Dalung yayi shiga irin ta ala'ada, waɗansu mabiyan shafukan sada zumunta suna ganin yin wannan shigar tashi a matsayin minista bai dace ba. Amman dai ya kamata jama'a su fahimci cewan ala'ada daban take da rike mukamin minista, duk girman mukamin ka ala'adan ka abun riƙewa ce kuma abar girmamawa, saboda haka masu chachakan minista game da wannan shigan nashi basu kyauta ma ala'adan shi ba sannan basu san girma da muhimmanci al'ada ba.
Comments
Post a Comment