Rashin Adalcin Duniya (2)
Rashin Adalcin Duniya (2) Idan mukayi duba akan lamarin satar yara 'yan makaranta da kungiyar Boko Haram ta sace su kusan 200 da 'yankai, inda hankali duniya ya karkata kan gwamnatin Nigeria domin ganin an ceeto wadannan yaran, inda har gwamnatin kasar mu Nigeria tayi tayin neman taimako daga manyan kasashen duniya kan ceto wadannan yaran 'yan makaranta. Duk dayake lamarin daya shafi tsaro lamari ne dake bukatan taka tsan-tsan da kuma boye wadansu surruka tare da amfani da kwararun jami'ai. Toh babban abundake daure mani kai shine yadda gangamin kungiyoyi ke fuskanta barazana a nan cikin gida Nigeria tare kuma da lafawar yawan gangamin da kungiyoyi ke shiryawa kan gwamnati takara matsa kaimi wajen ceto wadannan yaran. Kungiyar #BringBackOurGirls ta fuskanci barazana da wata kungiyar mai suna irin nata a Unity fourtune Abuja, wurin da suke taruwa domin isar ma gwamnati da sakon su, Inda lamarin ke daure mani kai akan ceewan su wadannan kungiyoyi idan har don Alla...