Posts

Showing posts from 2011

Boko Haram a Nigeria

Kungiyar nan da aka fi sani da suna BOKO HARAM a Nigeria wadda take da halhakib kaddamar da wadansu Harere da ake kaiwa a Nigeria, ta samu asali ne akan Rashin kishin Shugabanni da kuma rashin adalchi da Shugabanni ke yima wadanda dsuke Mulka. Haka kuma akwai Talauchi da rashin aiki yi fa ke damun Matasa a Nigeriam Babban Hanya bi a wannan matsalan da ke Damun kasar mu Nigeria shine aiwatar da Adalchi ga wadanda shugabanni ke mulka, tare da rashin nuna bamabachi ko kuma akida ga Al'umma, samar ma matasa aikin yi da kuma kula da tarbiyan matasa a cikin kasa suna daga cikin abubwan da gwamnati ya kamata ta kula dasu domin maganchi irin wadannan Kungiyoyin Kunno kai a cikin kasa Nigeria Kasa mai al'umma kimanin mutane Miliyan Dari da Hamsin (150.000000) baya ga haka kuma Nigeria itace kasar da tafi kowace Yawa a nahiya mu ta Africa, Kuma itace tafi kowace kasa yawan bakaken fata a duniya. Akwai babban aiki ga mahukuntan Nigeria domin magance wannan matsala ta Boko haram. Kungi...

Ahmad Mohammad Salisu: Ta'addanci a Nigeria

Ahmad Mohammad Salisu: Ta'addanci a Nigeria

Ta'addanci a Nigeria

''Sheikh: Wannan batu yana nan, mu darika ba ma kafirta kowa. Mun dauki kowa musulmi ne, amma su suna kafirta mu don kawai  ba mu shiga Izala ba. Mu babu ruwanmu da kafirta wani. Duk wanda ya kira kansa musulmi mun yarda da imaninsa, komai girman dan Izala idan ya kafirta mu to babu ruwanmu da shi. Hatta kafiri idan ya ganmu ya ga musulmi, idan ya ga iyayenmu ya ga musulmi, bai ma san darikarmu ba balle ya jawo ta, bai san  Shehu Tijjani ba balle ya zage shi. Kuma kafiri ba ya daura lasifika a coci ya yi mana rajamun kaulasan, haka a mota, don haka muka ce idan dan Izala ya tsaya zabe da wanda ba musulmi ba, aka rasa na uku sai dan Izala to mu wanda ba musulmin ba za mu zaba. Ba don komai ba saboda ba ya kafirta mu kuma yana cin yankanmu. Kuma ba ya zagin iyayenmu da malamanmu, to shi ya sa za mu zabi kirista mu bar dan Izala don bata mana suna da cin mutuncinmu da suke yi, suke kafirtamu.'' Shiekh Dahiru Usman Bauchi na daya daga cikin manyan malaman Wannan kasar, ...
SIYASAR MU A YAU Godiya ta tabbata ga Allah Subahanhu wata'ala daya bani ikon yin tsokachi ko ince fadakarwa a bisa abubuwan da suke faruwa ga SIYSAR MU A YAU. musamman a wannan lokichin da zabe ke kara karatowa a kasarsamu. Da farko abinda muka fahimta da siyasa shine, kusantar al'umma zuwa ga gwamnati, sannan gwamnati ta san mene matsalar al'ummarta, ta hanyar bamu damar mu zabi mutanen da muke tsammanin sune adilai a tare da mu, domin su shugabanche mu. to amman KASH!!! Shin wai jamma'a muna-nufin har yanzu bamu fahimchi ko mai-nene SIYASA BA? shin jama'a har yanzu bamu san adilin daya dace ya jagoranche mu bane? to ko son zuciya ne da rashin sanin ciwon kai ne ke damun mu? ya kamata mu chire kwadayi a tare da mu, mu farka daga magagin bracin da muke yi domin musan matsalolin da suke addabarmu. mu kore azzaluman shugabanni daga mulki, mu kori 'yan baradan su da azzaluman da ke goya masu baya, kai da ma duk wani wanda bai kaunan kawo cigaba a kasa...

GUGUWAR SAUYI A AFRICA (KAN MAGE YA WAYE)

ILIMIN ADDINI

Bissimillahi-Rahamanir Raheem. Godiya da dukkan Yabo sun Tabbata ga Ubangiji, Tsira da Aminchi Shugaban mu Annabin Rahama (S.A.W)... A yanzu muna cikin wani irin zamani ne, wanda har in baka da Ilimi to Bambanchi ka da jaki Bindi... Ilimin ZAMANI da kuma Ilimi na ADDINI su ke mai da mutum cikakken dan ADAM, To a wannan zamanin Ba'a dauki Ilimin ADDINI da muhimmanchi ba kamar yanda ake daukar Ilmin ZAMANI... Mai ne ya sa Haka? Ko don Ba'a Daukan ka aiki da Ilimi ADDINI? Ko dan ba Larabchi muke Amfani da shi bane a harakar mu na Yau da kullum ba? Ya Kamata Dukkan Muslmi ya tuna da Abin da ya zo yi Duniya (Wato Bautan Ubangiji) '...Kasan Allah kafin ka fara bauta mai...' Mafi akasarin Al-umman muslmi da ke Arewacin Kasar mu ta Nigeria, musamman ma tsofafin 'yan Boko, basa kulawa da Ilimin ADDINI kamar yanda suke kulawa da na Ilimin ZAMANI... Manzon tsira (S.A.W) ya umurce mu da mu je neman ilimi ko a ina ne cikin Duniya, Har ya kamanta muna da Ko nisan wurin ya kai K...