Posts

Gwamnatin Tarayya Zatayi Zama Da Kungiyoyin NLC Da Kuma ASUU A Yau

Image
A yau Litinin ne shugabannin kungiyar ƙwadago na Nigeria (NLC) zasuyi zama da gwamnatin tarayya domin samar da mafitar karshe akan yajin aikin da suke shirin zuwa wanda ya shafi mafi karanci albashin ma'aikata, ministan ƙwadago da kuma ministan kasafi da tsare-tsare game da ministan kudi na Nigeria sune zasu kasance manyan jagororin tattaunawan ta bangaren gwamnatin tarayya. Duk a yau din kuma, gwamnatin tarayya zata kara yin wani zama tare da ministan ilimi da kuma shugabannin kungiyar malaman jami'oin ƙasar nan domin ganin an kawo karshen yajin aikin da suka tsunduma kusan watanni biyu kenan, ana fatan kawo karshen wannan yajin aikin a yau.

Dan Sanda Ya Kashe Matasa Biyu A Benin

Image
Wani dan sanda da yayi tatul da giya ya kashe waɗansu matasa biyu a wajen murnan shigowar sabuwar shekara, lamarin ya faru ne a Kings square dake Birnin Benin ta Jahar Edo. Shidai jami'in tsaron yazo halba bindiga a sama ne domin murnan shigowar shekarar 2019 amman ya kuskure juya bindigan zuwa sama inda ya samu waɗansu matasa dake wurin ya bindige su, anan take daya daga cikin matasan ya sheka lahira, dayan matashin kuma ya cika ne bayan da aka gaza samun jami'an kula da lafiya da zasu iya bashi taimakon gaggawa.

Mata (11,0000) Yan Najeriya Ke Karuwanci A Kasar Italiya

Image
Kimanin yan mata matasa dubu goma sha daya (11,0000) aka tsallaka dasu kasar Italiya domin yin aikin karuwanci a shekarar 2016 kawai, wannan kiyatsin ya fito ne daga jaridar Economist, ta wallafa wannan adadin ne a shafinta na twitter. Sau dayawa dai ana fitar da yan mata matasa zuwa kasashen ketare da sunan nema masu ayyukan yi inda akarshe ake ake saka su a hanyar karuwanci da kuma bauta.

Minista Sanye Da Kayan Ala'ada

Image
Ministan matasa da wasanni Barrister Solomon Dalung yayi shiga irin ta ala'ada, waɗansu mabiyan shafukan sada zumunta suna ganin yin wannan shigar tashi a matsayin minista bai dace ba. Amman dai ya kamata jama'a su fahimci cewan ala'ada daban take da rike mukamin minista, duk girman mukamin ka ala'adan ka abun riƙewa ce kuma abar girmamawa, saboda haka masu chachakan minista game da wannan shigan nashi basu kyauta ma ala'adan shi ba sannan basu san girma da muhimmanci al'ada ba.

Tsohon Shugaban Kasar Nigeria Alhaji Shehu Shagari Ya Rasu

Image
Allah yayi ma tsohon shugaban ƙasa Nigeria Alhaji Shehu Shagari rasuwa a yau juma'a a asibitin tarayya dake Birnin Abuja, ya rasu yanada shekaru 93 a duniya. Gwamnan Jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ne ya sanar da mutuwan tsohon shugaban kasan a shafin sa na Twitter. Allah ya jikanshi da rahamarsa.

Zan Kawo Karshen Kashe-Kashen Zamfara Cikin Wata Daya - ATIKU ABUBAKAR

Image
Dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya fitar da dubarun da zai dauka domin ganin kawo karshen matsalar tsaro a jahar Zamfara. A cikin sakon hoton video daya fitar a shafinsa na twitter yace, “Alummar Jahar Zamfara ina tare daku a cikin wannan yanayin da kuka tsinci kanku a hannun mahara wadanda suke sace dukiyar ku kuma suke kashe maku al’umma tare da barnatar maku da dukiyoyin ku” Zuciya na tana kadawa sosai akan yanayin da kuka tsinci kanku in addua’an Allah ya kawo maku karshen wannan kashe-kashe da kuma irin wahalar da kuke ciki” "Ni dan takaran shugabancin Kasar nan ne, ina mai tabbatar ma al’ummar jahar Zamfara cewan idan har kuka zabe ni a matsayin shugaban Kasa a ranan 16 ga watan February 2019 bazan zarce wata daya ba da shan rantsuwan kama aiki ba zan turo rundunar zaratan jami’an tsaron na sojoji da yan sanda dubu talatin (30.000) domin su fatattaki wadannan yan ta’adan da suke kashe al’umma a Jahar taku." "A lokacin zaben ...

Wadansu matasa a garin Enugu sun kone motar kampen na APC

Image
Wadansu matasa a garin Enugu sun kone motar kampen na mallakin Jam'iyyar APC kurmus, Dan takara Honourable Benjamin Nvute wanda yayi magana da manema labarai yace "Motar wacce aka lullube da hotunan yan takara Senator Ayogu Eze, Prince Lawrence Ezeh da kuma na shugaban kasa Muhammadu Buhari itace motar da jamiyyar ke amfani da ita wajen ayyukan ta na kampen a karamar hukumar Nkanu" Motar wacce aka barta wurin mai gyara dauke da wadansu takaddu masu muhimmanci wadanda suka shafi ayuukan jam'iyyar da kuma na kampen, yazo ya tarar da ita a kone kurmus. A Jahar dai ta Enugu akwai matsalolin yage-yagen hotunan yan takara tare da allunansu wanda haka yasa masan ke nuna tsoron su aka yanayin siyasar ta Jahar Enugu.