Masarautar Kano

Da fatan mun wayi gari cikin koshin lafia
Marasa lafia daga cikinmu Muna rokon Allah ya basu lafia, mu kuma da mukeda lafiar mun rokon A;;ah ya kara muna lafiyar.

Duk dayake Allah bai bani iko nayi rubutu akan abubwan da suke faruwa a masarautar Kano ta nadi sabon sarki mai martaba malam Sanusi Lamido Sanusi ba, cikin ikon Allah yau na samu daman da zan danyi tsokaci akan jita-jitar da jama’a ke yadawa a cikin garin Kano da kuma yawancin shafukan sada zumunta musamman ma na facebook.

Kamar yadda muka sani ne cewan a al’adance babu rowan shugaban kasa kan lamarin daya shafi nadin sabon sarki a kowace masarauta kowa, barre har shi shugaban kasar ya samu daman tsige sarkin ko wani basarake kokuma yayi masa wata barazana, duk dayake akwai rawar da gwamnoni suke takawa wajen nada sabon sarki da kuma tafiyar da wadansu harkoki na fada.

Ya kamata jama’a mu san cewan shugaban kasa bashida hurumin dakatar da koda sakamakon zabe ne da hukumar zabe ta rigaya ta fitar barre kuma dakatar da nadin sabon basarake, ko mai unguwa bai da izinin dakatarawa.
Ya kamata jama’a musa tsoron Allah a zukatanmu, mudaina bari wadansu bara gurbi suna amfani damu wajne yayata labarai na karya wadanda zasu iya janyo tashin hankali.
Gaba daya gidan sarautar ta Kano dangin juna ne, kamar yadda shi kanshi mai girma Sarki ya bayyana a cikin wani jawabinsa, ya kuma kara da cewan duk wata tashin hankali da zata biyo baya saidai inda ga waje ne, wato saidai idan an dauko wasu an biyasu domin su kawo wani tashin hankali, amman ba dai daga gidan sarautar ba.
Jama’an Kano ya kamata ku lura da irin illar da hayaniya zata iya jefa yankinku dama Nigeria baki daya, da kuma irin koma baya da zaku maida kanku kasancewar Kano itace cibiyar kasuwancinmu na arewa.
Sabon sarkin Kano mai martaba Malam Sanusi Lamido Sanusi shine sarkin Kano a yanzu kamar yadda majiya mai tushe ta bayyana a ranar Lahadin data gabata.
Sannan kamar yadda yake ga al’adan masarautar Kano, duk wadansu manyan shaida da kuma kayyakin na masarautar wadanda suke tabbatar da sarauta, an mika wa sabon sarkin maimartaba malam Sanusi Lamido Sanusi.

A karshe ina rokon Allah ya tashi riko, ya kuma tsare Kano da Nigeria baki daya.
Ameen.

Comments

Popular posts from this blog

Minista Sanye Da Kayan Ala'ada

Zan Kawo Karshen Kashe-Kashen Zamfara Cikin Wata Daya - ATIKU ABUBAKAR

Fashin Bakin Jawabin Shugaban Kasa