INNALILLAHI WANNI-ILAHIR RAJI’UN!

Misalin karfe 7:37 na yamma ne 13/6/2014 ranar juma’a ina zaune ni kadai, sai ga kiran waya daga wata bakuwar number ta Airtel, ashe wannan kiran daga daya daga cikin abokanaina ne ya kira ni domin shaida mani rasuwar abokinmu Husaini Aliyu Nakofa.
INNALILLAHI WANNI-ILAHIR RAJI’UN!

Lallai nayi babban rashi aboki na rasuwa Husaini Aliyu Nakofa, abokin zama ne kuma ‘dan uwa na kwarai mai kula da addini, sannan ga hakuri da sanin girman mutane tare dashi, mutum ne mai son zumunci tare da ziyaran abokanai kowane lokaci, akwai natsuwa da kuma iya zama cikin mutane.

Hussaini Aliyu Nakofa mutum ne mai kula da addini, baya wasa da lamarin daya shafi addini musamman ma salah, A duk lokacin da Husaini Aliyu ya rasa Sallah Asuba cikin jam’I, idan muka fito wurin aiki yakan nuna mani damuwarsa sosai kan rashin samun sallah asuba cikin jam’I da baiyi ba, Hussaini Aliyu Nakofa mutum ne mai kokarin yin azumi na nafila tare da kokarin ganin ya faranta ma mahaifiyarsa rai kowane lokaci.
Kowane lokaci yakanso yaganshi kusa da mahaifiyyarsa, hakanma yasa a cikin dakin mahaifiyyar nasa yayita jinya har saida lokacinsa yayi, wato har saida Allah ya dauki ran nashi a cikin dakin mahaifiyar nasa.

Duk daya ke Husaini Aliyu Nakofa ya dauki lokaci mai tsawo yana jinya kan rashin lafiyar data zama ajalinsa, rasuwar nashi ta girgiza Jama’a da dama, musamman ma mu matasa abokananshi.

Shekaru biyu da suka wuce kenan da Marigayi Hussaini Aliyu yayi yunkurin yin aure, amman Allah bai tabbatar da nufin auren ba, Allah ya dauki ran Hussaini Aliyu Nakofa da babban burin na yin aure a ransa, kafin rashin lafiyar data zama sanadiyyar rasuwasa tayi karfi, saida Hussaini yaga yayi kokarin kamala wurin da zai zauna idan Allah ya nufeshi da yin aure,
Allah mai iko! Ashe Hussaini bazaiyi aure ba, haka zai koma ma Allah.

Ina rookon Ubangiji Allah ya jikan Husaini Aliyu Nakofa da rahamarsa ya sanyaya kabarinsa ya kuma haskaka kabarin nasa, mu kuma idan namu lokaci yayi muna rokon Allah ya mu cika da imani.

Ameen

Comments

Popular posts from this blog

Minista Sanye Da Kayan Ala'ada

Zan Kawo Karshen Kashe-Kashen Zamfara Cikin Wata Daya - ATIKU ABUBAKAR

Fashin Bakin Jawabin Shugaban Kasa