INNALILLAHI WANNI-ILAHIR RAJI’UN!
Misalin karfe 7:37 na yamma ne 13/6/2014 ranar juma’a ina zaune ni kadai, sai ga kiran waya daga wata bakuwar number ta Airtel, ashe wannan kiran daga daya daga cikin abokanaina ne ya kira ni domin shaida mani rasuwar abokinmu Husaini Aliyu Nakofa. INNALILLAHI WANNI-ILAHIR RAJI’UN! Lallai nayi babban rashi aboki na rasuwa Husaini Aliyu Nakofa, abokin zama ne kuma ‘dan uwa na kwarai mai kula da addini, sannan ga hakuri da sanin girman mutane tare dashi, mutum ne mai son zumunci tare da ziyaran abokanai kowane lokaci, akwai natsuwa da kuma iya zama cikin mutane. Hussaini Aliyu Nakofa mutum ne mai kula da addini, baya wasa da lamarin daya shafi addini musamman ma salah, A duk lokacin da Husaini Aliyu ya rasa Sallah Asuba cikin jam’I, idan muka fito wurin aiki yakan nuna mani damuwarsa sosai kan rashin samun sallah asuba cikin jam’I da baiyi ba, Hussaini Aliyu Nakofa mutum ne mai kokarin yin azumi na nafila tare da kokarin ganin ya faranta ma mahaifiyarsa rai kowane lokaci. Kowane lo...