Taron Mjalisar Dinkin Duniya 68th
A jiya talata ne majalisar dinkin duniya ta bude taronta wanda tasaba yi duk shekara-shekara karo na 68 th a babban ginin majalisar dake birnin New York na kasar America Taron yazo ne dai-dai lokacin da kasashen yamma suke nuna ma kasar Syria yatsa akan zargin da akeyma gwamnatin kasar na amfani da makamai masu guba a yakin basasan da ya kusa kwashe sekaru 3 ana gwabaza da ‘yan tawayen kasar . Akuma dai dai lokacinda ake ci gaba d a cacar baki tsakanin Amurka da Rasha, kan wanda za'a azawa alhakin kai hari da makamai masu guba a Syria . Hakanan kuma an fara ganin alamun Iran ta fara sassautowa daga tafarkin fito na fito da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyar d a ake zargin tana fakewa da shi ne domin habaka makaman nukiliya. Haka kuma akwai batun yaki da ta’addance da kasahsen duniya suke ikararin sunayi a duniyar, inda wannan zaman yazo dai-dai da lokacin da kungiyar Al-Shabab ta kaddamar da wani hari a birnin nairobi na Kenya. Haka kuma...