FATAWOYIN AIKIN HAJJI DA UMRAH DA ZIYARA (1)
FATAWOYIN AIKIN HAJJI DA UMRAH DA ZIYARA (1) Na SHAIKH ABDULWAHAB BIN ABDILLAH ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ ﻭ ﺻﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺍﻟﻜﺮﻳﻢ 1. Tambaya: Menene ma’anar Hajji? Amsa: Ma’anar Hajji a harshen Larabci shine nufin wani abu. Amma ma’anar Hajji a shari’ance shi ne nufin ziyarar dakin Allah (ka’aba), bisa girmamawa, da wasu kebantattun ayyuka (na ibada), a kebantaccen lokaci, kuma a wani kebantaccen wuri 2. Tambaya: Menene falalar aikin Hajji? Amsa: Aikin Hajji yana da falala da yawa. Kadan daga ciki shi ne: · An karbo Hadisi daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) yace, Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Aikin Umrah zuwa wata umrar, yana KanKare zunuban da ke tsakaninsu. Haka kuma Hajji Mabrur , ba shi da sakamako sai aljanna". · Haka kuma an karbo Hadisi daga Ma'iz (Allah Ya yarda da shi) ya ce: An tambayi Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) cewa: Wadanne ayyuka ne suka fi falala? Sai ya ce: "Imani da Allah Shi kadai, s...