Posts

Showing posts from January, 2019

Gwamnatin Tarayya Zatayi Zama Da Kungiyoyin NLC Da Kuma ASUU A Yau

Image
A yau Litinin ne shugabannin kungiyar ƙwadago na Nigeria (NLC) zasuyi zama da gwamnatin tarayya domin samar da mafitar karshe akan yajin aikin da suke shirin zuwa wanda ya shafi mafi karanci albashin ma'aikata, ministan ƙwadago da kuma ministan kasafi da tsare-tsare game da ministan kudi na Nigeria sune zasu kasance manyan jagororin tattaunawan ta bangaren gwamnatin tarayya. Duk a yau din kuma, gwamnatin tarayya zata kara yin wani zama tare da ministan ilimi da kuma shugabannin kungiyar malaman jami'oin ƙasar nan domin ganin an kawo karshen yajin aikin da suka tsunduma kusan watanni biyu kenan, ana fatan kawo karshen wannan yajin aikin a yau.

Dan Sanda Ya Kashe Matasa Biyu A Benin

Image
Wani dan sanda da yayi tatul da giya ya kashe waɗansu matasa biyu a wajen murnan shigowar sabuwar shekara, lamarin ya faru ne a Kings square dake Birnin Benin ta Jahar Edo. Shidai jami'in tsaron yazo halba bindiga a sama ne domin murnan shigowar shekarar 2019 amman ya kuskure juya bindigan zuwa sama inda ya samu waɗansu matasa dake wurin ya bindige su, anan take daya daga cikin matasan ya sheka lahira, dayan matashin kuma ya cika ne bayan da aka gaza samun jami'an kula da lafiya da zasu iya bashi taimakon gaggawa.