AMERICA DA BOKO HARAM
BOSTON, MA  — Babban kwamandan Rundunar  Sojojin Amurka a Afirka, Janar David Rodriguez, yace sojojin Amurka su  na sanya idanu sosai a kan take-taken ‘yan Boko Haram na Arewacin  Najeriya, a yayin da kungiyar take fadada huldarta da wasu kungiyoyin  ta’addanci dake nahiyar Afirka.   Janar Rodriguez, wanda ya karbi ragamar shugabancin wannan runduna da  ake kira AFRICOM a takaice, wadda kuma ta ke da hedkwata a Stuttgart  dake kasar Jamus, yace daya daga cikin babban abinda suka bayar da  muhimmanci gare shi, shi ne yaduwar kungiyoyin tsagera a Afirka. Yace  musamman ma, sun sanya idanu a saboda damuwa da suke da ita ta musamman  kan kungiyar Boko Haram a saboda a wani bangare, kungiyar tana ci gaba  da fadada huldarta da kungiyoyin ta’addanci na yankin.   Ya ce, “mun damu da wannan domin irin wannan hulda tana fadada dama da  fadada kwarewa ga irin wadannan kungiyoyi, kuma mun san Boko Haram  kungiya ce mai son zub da jini sosai. Kungiya ce da ta ke yin illa ga  yankin arewacin Najeri...